ƘADDARA TA RIGA FATA: Fita Ya 22
NA MARUBUCIYA:-
AUNTY NICE
@wattpad AuntyNice.
SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-
NABEELAH ARABI
NUHU ARABI
SHAFI NA 22
__📖 Babu ɓata lokaci muka shiga bedroom ɗinmu muka fara haɗa kayan mu, muna cikinyi akayi azahar, muna idar da sallah Dr ya ƙirani a waya yace, “Baby kije bakin gate akwai masinjan mu ya kawo muku abinci, don Allah kiyi haƙuri har yanzu bamu gama case ɗinnan ba”, haƙuri na bashi sannan na mishi godiya.
Wajen gate ɗin na fito na karɓi ledan da aka mana take-away ɗin, na shigo haraban gidan muka haɗu da Peter da David, murmushi suka fara mun, Peter kuma yana harara na da wasa, domin fuskanshi ɗauke yake da murmushi, “preety wato Dr ya ɓoye mana ke ko”? Ya faɗa yana duban ƙofan gidan Dr.
Dariya David yayi yace, “ba dole ya ɓoye mata mai kyau ba, kaga laifin shi ne bros”? Nima dariya nayi ganin sun harbo jirgin mu, ina duban su nace, “baku fahimta bane Dr ba soyayyah muke yi da shi ba, yayah nane fah”.
Dariya sukayi suna kallon junan su, peter yace “mun yadda ba soyayyah kukeyi ba, amma yau meye ake faɗa a depertment ɗin mu? Ko ina ka tsaya guys sai labarin tashin hankalin da Dr yayi akan ki ake tayi, toh duk wannan ma ba soyayyah bane ko”? Zaro ido nayi na juya ina dariya nayi hanyan side ɗinmu, suma dariya sukeyi suna cewa na gudu don naji zasu faɗi gaskiya.
Barin duk abinda mukeyi na shirin kayan mu mukayi, muka zauna muka ci abinci, da yake dama yunwa mukeji, muna gama ci muka ɗauko apple juice da mukayi tun daren jiya muka sha, kallo na Amaal tayi tace, “nikan bacci zanyi kafin la’asar” ta miƙe tayi hanyar bedroom, nima tashi nayi na bi bayan ta.
Bamu muka tashi ba sai wurin 5:00pm, saboda rashin bacci da bamu samu kwana biyu ko alarm bamu ji ba, da sauri mukayi sallan, sannan Amaal ta kalle ni tace, “Hummy yau kam muhuta ɗaura abinci, kawai musha cornflakes da dare, don wallahi duk wani ciwon jiki nake ji, addu’a na ɗaya musamu mu bar ƙasan nan lafiya ciwo na bai mutsa ba”, ta faɗa tana daddana ƙafan ta da kanta.
Duban ta nayi nace, “Dr fah me zai ci kike nufi”?
Harara na tayi tace, “sai yaje yayi abinda ya saba tun da chan baya”, ta fara tana dubana da dariyan tsokana.
Turo bakina nayi gaba nace, “ke kika sani bari yazo na gaya mishi, kuma babu inda zaki bimu idan yace muje shan ice cream”, na faɗa ina tashi tsaye don zuwa na duba abubuwan da suke kitchen ɗin mu.
Dab za’ayi sallan magrib Dr Hussain ya dawo, knocking gidan mu yayi, da sauri kaman jiranshi na keyi naje na buɗe, tsayawa yayi yana dubana da murmushi a fuskar shi, nima mayar mishi nayi, sannan na bashi hanya ya shigo ciki.
Yana zama na wuce kitchen na haɗo mishi sauran cake ɗinmu da apple juice mai sanyin daɗi, gefen shi na samu na xauna ina zuba mishi juice ɗin a cup.
Sai bina da kallo yake yana murmushi, a hankali nace, “Dr nah me yake saka ka farin ciki bayan gobe zan yi maka nisa”?
Dariya yayi mai ɗan sauti sannan ya dube ni yace, “ina farin cikin hukuncin da akayi wa Dr Khadijah ne kawai baby, kinsan an mata doka mai tsanani akaina da ke baki ɗaya, kuma management sun tabbatar mata da cewa idan har ta sake maimaita makamancin irin haka zasu dakatar da ita, kuma tayi mugun razanan, don har aka tashi a taron bata daina sha re hawaye ba”, ya faɗa yana ƙara murmushin kan fuskan shi.
Ina kallon shi da mamaki, “Dr mu toh meye yake saka ta kukan”? Yama ajiye cup ɗin bayan ya shanye wanda na zuba mishi ya dube ni yace, “Ni wallahi baby har tsoron irin son da Khadijah ta keyi mun nakeji, kinsan bayan ance ta bani haƙuri, saida ta ban tausayi, domin a hankali babu maiji tace, zan bar ƙasan nan tabbas sabida kai Dr, domin zuciyata bazata ɗauki ganinka da wata ba bayan ni”, Ya faɗa yana dariya.
Wani iri naji cikin zuciyata, domin ko babu komai macece ƴar uwata, kawar da maganan nayi ina duban shi nace, “Baby nah yau kaman mun gajji, ko zakayi take-away ne da dinner kaci? Muma cornflakes kawai zamu iya sha duk muna jin gajjiya yau a tare da mu”, na faɗa ina duban shi da alaman damuwa a fuskana.
Shima turo baki yayi yana kwaikwayo na yana buga ƙafa a ƙasa yace, “nikan bazan yadda ba, yau abincin Baby zanci, ni wallahi bazan yadda da wayon nan ba”, dariya muka farayi ni dashi a tare, ina kallon shi nace, “haba baby ni da yakamata nayi shagwaɓa sai kaine yau zakayi, toh ni yayah zakayi dani idan kai kanayi”?
“Kawai sai a raba kowa da turn ɗin yin sakalcin shi, idan nayi na 2dys sai kema kiyi na 2dys, kowa yayi ta fama da ɗan uwan shi ko ba haka ba”? Dariya nayi na miƙe ina cewa, “bari naje kitchen ɗin na duba me zan dafa maka”.
Da sauri ya kamo hannu na bayan shima ya tashi ya tsaya, dab da bayana yazo ya tsaya kaman wanda zai jinginu da ni a hankali yace, “Baby nah bana son ki wahala, kawai ki gayawa Amaal idan anyi ishaa zamu fita muci abinci ko, bana son ƴar baby nah ta wahala”, ya faɗa yana ɗaura haɓan shi a kafaɗa na, da sauri naja jikina na shige bedroom ɗinmu da gudu, dariya ya fara yi yana girgiza kanshi, ya juya ya fita a gidan, sai da na tabbatar ya bar parlon tukun na fito na rufe ƙofan na ƙoma bedroom wurin Amaal.
Zama nayi ina ajiyar zuciyar mai ƙarfi, juyowa tayi tana hararah na tace, “zakuji da shi dai magulmata”.
Murguɗa mata baki nayi ina jujjuya mata ido nace, “ki shiryah anjima zamu fita dinner da Baby nerh”!
Hararana tayi tace, “sai ki fita da Babyn ki, nima Hubby nah zai zo mufita yawon sallama kafin ya iso ni a DAMMAM“.
Zaro ido nayi ina dubanta, “laillai yarinyar nan wuyanki yayi kauri, toh babu inda zaki tafi da shi ke kaɗai, Ummi idan ta samu labari ranta zai ɓaci, saidai yaxo mu fita tare dukkan mu, ina gadinki kina gadina”, na faɗa ina rawan india a gabanta.
Gaba ɗaya daga ni har Amaal ƙamshin daɗi mukeyi, gashi munyi shigan wasu english wears masu masifar kyau, munyi rolling kanmu da wani gyale mai kyaun gaske, nawa colour red and green, na Amaal kuma red and black, haka muka fito muka shiga bayan motan Dr Hussain, inda shi kuma da Dr Abdallah suna gaba.
ranan munyi yawo kam bayan mun ci abinci, har wurin 11:00pm tukun muka je muka sauƙe Dr Abdallah, sannan muka dawo namu gidan, Amaal sallama tayiwa Dr nah ta wuce ciki, mukuma muka zauna a parlon, ƙura mun ido Dr yayi, ni kuma ganin kallon bana ƙare bane sai na matsa nesa da shi ina ta kame-kamen abinda zance, don gaskiya ni bana son irin kallon da yake mun.
“Baby yanzu gobe kenan zaku gudu ku bar ni ko”? A hankali na dube shi ganin yadda yayi mun maganan kaman bazai buɗe bakin shi ba, juyar da kaina nayi na bar duban shi, nima murya cikin nutsuwa nace, “Baby ko na zauna ne nayi hutun anan tare da kai”?
“Ban isa ba baby, ki tafi kawai nima xan fi so naga kin samu masu ɗebe miki kewa”, haka mukayi ta hira, da ƙyar muka rabu wurin 12:30pm, bayan ya tafi na shigo ɗaki, baki a buɗe nake kallon Amaal da mamaki, ta wani bararaje akan gado sai wani luv ta ke kwasa a waya ita da Dr Abdallah, ganin haka na wuce toilet nayi wanka nazo na kwanta ina ta ja mata tsakin sun dame ni.
Saida mukayi wanka muka saka kayan mu tukun aka ƙira sallan asuba, jirgin mu 9:00am zai tashi gashi airpot ɗin da nisa shiyasa muka tsayar 6:00 zamu fita domin tafiya, tunda muka shiryah nake ji kaman nayi kuka saboda tafiyan da zanyi na bar Dr nah shi kaɗai, a haka jiki a sanyaye muka shiryah.



