SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-
NABEELAH ARABI
NUHU ARABI
SHAFI NA 27📑
__📖 Amaal ce ta shigo ta sa me ni nayi nisa cikin tunani, maka mun duka tayi a lap ɗina tana hararana da wasa tace,
“a haka kaman kina son Dr, amma kuma ƙasan zuciyar ki tsantsan yaudara ne”.
Tashi na yi zaune ina sosa inda ta maka mun marin nace,
“amma kina aikata babban saɓo Amaal, ni kike gayawa bana son Dr? to ki gaggauta zuwa ki kuskure bakin ki a toilet, don kin yi mun babban laifi wanda ya kai na miki hukunci”.
tashi nayi na miƙa mata hannuna alaman ta riƙe ni na miƙe tsaye.
Hararana tayi ta neme wuri ta zauna,
“gaskiya Hummy ki daina kula Faisal, ni na haɗa ku ne don Dr ya razana ya ƙara baki muhimmanci, yasan ba shi kaɗai bane, amma ke kuma sai kina son wuce gona da iri, gaskiya ki canja tsari”.
ta faɗa kaman za tayi kuka.
Dariya nayi mai ɗan sauti, “Amaal wallahi bana tunanin akwai wani namiji da zai juyar mun da hankalina akan Dr, babu shi saboda haka kima manta da maganan Faisal, zan kula da wannan”.
Faisal gaba ɗaya ya saka na daina zaman cikin ɗaki, saboda babu hali nayi wasu mintuna zaka ganshi ya shigo, kuma babu inda yake dosa sai kan bed inda nake zaune ko nake kwance, ganin haka da yake yi naji duk hutun ya fita mun a rai, saboda haka kullum ba zaka rasa ni a kitchen wurin Ummi da masu aikin gidan ba, ko kuma ina parlor ko ɗakin Ummi, abin haushi kuma babu hali yaga ina waya da Dr zai fara ƙoƙarin kai hannun shi jikina, ni kuma idan naga haka na gwammace na kashe wayan na bar wurin, wanda hakan yake saka ran Dr nah yana ɓaci.
Ranan da Faisal yayi 3weeks da zuwa Ummi ta fara mishi maganan komawan shi school, amma firr yaron nan ya ƙafe shi bazai tafi ba sai ranan da zamu tafi.
“Kasan dai hutunka ya ƙare, su kuma sauran 1week, to ina ruwan ka da zaman su ne kam Faisal?”.
Ummi ta faɗa tana duban shi.
“Ummi gaskiya ni na gaya miki auren Hummy nake sonyi, to ya ya za’ayi nabarta ita kaɗai ni kuma na tafi? gaskiya ni sai ranan da zasu tafi tukun na tafi”.
ya faɗa da wani yanayin shagwaɓa.
“Hmmm ka gamu da wahala wallahi, na gaya maka Humaira akwai wanda ta ke so, me yasa kake da son haɗa fitinane? kawai ka kama hanyar komawa ko na haɗa ka da Abbu”.
Ummi ta faɗa tana binshi da harara.
Dariya ya yi ya tashi ya fita a ɗakin, yabar Ummi da mamakin yaushe Faisal ya canja hali haka ne wai kam?.
“Baby mai kake so na shirya maka? Kasan daɗin da nake ji kuwa yau?”.
na faɗa mishi cike da jin daɗin wai gobe zai zo, idan munyi 5dys sai mu juya tare da shi, shi dai bai faɗa mun abinda yake so ba sai dariya na da yake ta yi.
Ranan tun safe Ummi ta saka mu tashi muka fara aikin abinci domin zuwan Dr, ni dai banda farin ciki babu abinda na keji, sai snacks muke ta haɗawa iri da kala, wasu bamu soyawa ake saka su kawai a friedge, ga wani ƙaton cake da Amaal tayi baking ɗinshi, yayi matuƙar kyau sosai an rubuta sunan shi a jiki, ni dai sai farin ciki kawai na keyi.
Driver ne ya ɗauke mu nida Amaal domin tafiya taryo Dr, lokacin da mukayi ido biyu da shi sai da naji gaba na ya faɗi, domin ganin irin raman da yayi, amma ya yi kyau sosai, tsabar farin ciki bansan lokacin da na tafi da gudu na rungume shi ba, shima tsabar murnan ganina rungume ni yayi ƙamƙam a jikin shi, ita kuwa Amaal tana tsaye a inda ta ke sai murmushi ta keyi cike da tausayin mu, don daga ganin mu kaman mun shekara dayawa ba muga juna ba.
Da ƙyar ya iya ɗago da fuskana yana murmushi domin ganin murnan da nake yi ya koma zuban hawaye, yana goge mun hawayen yana fitar da na shi, murya a hankali yace,
“to ba gani nan na zo ba, kiyi shiru ana kallon mu fa, kada wata balarabiya ta ƙyasa miki babyn ki”.
ya faɗa yana sauƙe hancin shi kan nawa.
Buga ƙirjin shi nayi da ɗan ƙarfi nace,
“ni kan babu mai sonka sai ni ɗaya, kuma kai baby nane ni kadai, baby naji daɗi dana ganka, nayi mssn ɗin ka sosai”.
shi dai murmushi yake tayi yana matsamun kafaɗa na bayan ya ɗaga idon shi daga kaina ya dubi Amaal wanda tayi saurin share hawayenta, tana murmushi ta ƙara so inda muke tsaye.
Bag ɗin hannun shi ta karɓa, tana mishi sannu da zuwa, shima miƙa mata yayi yana tambayanta ya ya su Ummi? Bayan sun ɗan gaisa ne yana riƙe da hannu na muka wuce wurin motan.
Gaskiya su Ummi sun yi mishi kyakkyawan tarya, daga Ummi har Abbu sun nuna jin daɗin zuwan Dr, bayan ya huta yaci abinci, sai ya gaya musu zaije ya nemi masauƙi, duk yadda su Ummi suka yi dashi ya zauna anan gidan firr ya ki amincewa, babu yadda suka iya haka suka barshi driver ya kai shi wani hotel da yake kusa da gidan su, banji daɗin ƙin zaman da yayi ba, amma da muka fito domin yi mishi rakiya, yana riƙe da hannuna muna tsaye a jikin motan ya ƙura mun ido, don sai wani shagwaɓa nake ta sauƙe mishi akan banji daɗin ƙin sauƙan da yayi anan ba.
shi dai dariya kawai yake yi baice mun komai ba, can sai ga Faisal ya fito daga side ɗin shi, tunda ya ganmu tsaye da Dr ya wani ja birki yana kallon mu cike da mamaki, ganin haka ya saka Dr ya ƙara riƙe hannu na gam.
Tafiya kaɗan Faisal yayi ya iso inda muke tsaye, ina tunanin zai wuce amma kawai sai yaja ya tsaya yana bin Dr da kallon banza,
“Me ya fito da ke waje wurin wani bayan kin san ina sonki?”.
ya faɗa yana ƙoƙarin saka hannu ya jawo ni.
Murmushi Dr ya yi ya maida ni ta ɗayan side ɗinshi ya rungume ni sosai a jikin shi, nima da sauri na saka hannuna duka biyu na rungume shi, hannu Dr ya miƙa mishi alaman su gaisa, amma Faisal tsaki yaja mishi yana duban idon Dr yace.
“Yayah zaka shigo har gidan iyaye na kuma ka rungume matar da zan aura a gaban ido na? Kasan duk wani abinda na maka kai kajawo”.




