Zargin Batanci Ga Annabi: Kotu Ta Tsare Dokta Idiris Bauchi a Gidan Yari

Zargin Batanci Ga Annabi: Kotu Ta Tsare Dokta Idiris Bauchi a Gidan Yari

 

Wata kotun Majistare dake Bauchi ta bada umurnin a tasa keyar Dokta Idris Abdulaziz, Dutsen Tanshi malamin addinin Musulunci a Bauchi a  bisa zargin Public disturbance ("hargitsin jama'a da tayar da hankalin jama'a.") 

Majiyoyi da ga Rundunar Yansanda na jiha, da Hukumar Shariar Musulunci na jiha da kuma Almajiran Malamin sun tabbatar da tsare Malamin agidan gyaran hali.
Kwanakin baya wadansu kungiyoyin addini guda 17 karkashin kungiyar  Fityanul Islam ta Najeriya, ta  rubuta takardar koke ga kwamishinan 'yan Sandan jiha, bisa zargin cewa Malamin ya yi batanci ga Manzon Allah(S. A. W).
 Wassu daga cikin almajiransa sun ce Dokta Abdulaziz  a ranar Litinin ya amsa gayyatar ‘yan sanda kafin a gurfanar da shi a gaban kotu kan zargin da ake masa.
Majiyar ta ce  'yan sanda sun gurfanar da malamin ne a babban kotun majistare mai lamba 1. 
Alkalin kotun ya hana  belin Dakta ya bayar da umarnin a ajiye wanda ake tuhuma  a gidan gyaran hali.
Za  sake dawo dashi gaban kotu ranar Talata, kamar yadda wasu majiyoyi  suka sheda ma manema labarai.