Zanga-zanga: An ɓarnata kayan gwamnati a Sakkwato

Zanga-zanga: An ɓarnata kayan gwamnati a Sakkwato
Ɗimbin matasa sun fita zanga-zanga lumana a jihar Sakkwato domin nuna rashin gamsuwa kan halin yunwa da matsi da mutanen Nijeriya suke ciki.
Matasan sun yi ɓarna a kayan gwamnati inda kan titin Ahmadu Bello aka lalata wayar da ke tsakiyar hanya, a titin Sarki Yahaya an yi wa gwamnati ɓarna.
Mutane da dama sun yaba wasu matasa da suka yi zanga-zangar cikin lumana ba tare da taɓa kayan gwamnati da jama'a ba.
Matasa sun yi fitar kwari da ɗimbin yawan abin da ke nuna samun goyon baya a zanga-zangar da aka gudanar a Nijeriya.