Dan takarar Gwamnan Zamfara a jam’iyar ADC Honarabul Bilyaminu Yusuf Shinkafi ya yi alqawalin kare dokokin shari’ar musulnci a jihar Zamfara in ya samu nasara don ganin an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali da cigaba.
Bilyaminu Shinkafi a wata ziyara da yakaiwa malamin addinin musulunci Shaikh Tukur Jangebe a ranar Jumu’a cikin garin Gusau ya ce “a wannan yanki namu na Arewa Malamai su ne jagororinmu, shi ne dalilin da ya sa muka zo majalisin malam don mu jaddada biyayarmu ga Malam da neman a riqa ba mu shawara a duk in da muka kasa a yanzu da kuma in mun samu nasara, a kuma cigaba da yi mana addu’a.
“Malamai ku ne fitila da za ku haska mana da ba mu goyon baya, mu ‘ya’yanku ne ko bayan mun samu nasara za mu ci gaba da zama ‘ya’ya da neman shawara.
“Maganar shari’ar musulunci wajibi ce a matsayinmu na musulmai da suka yi imani da addinin musulunci, idan Allah ya ba ka dama akwai abin da ake tsammaninka ka yi, da wannan nake ba da tabbacin duk wani haqqi na shari’a za mu yi gwargwadon hali a gwamnatance wurin kare shi.
“Za mu cigaba da tuntuvar malamai domin samar da maslaha na komawa kan tsari na Allah domin Allah ya tausaya mana ya dawo mana da jihar mu cikin hayyacinta,” Kalaman Bilyaminu Shinkafi.
Zamfara tana cikin jihohin Arewa da ke fama da matsalar tsaro a tsawon shekarru in da ‘yan siyasa ke ta yin alqawalin samun nasarar magance matsalar har yanzu haqar ba ta cimma ruwa ba.






