Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya yi alkawarin dawo da tallafin man fetur bayan an shawo kan matsalar cin hanci da rashawa a kasar.
Obi ya bayyana hakan ne a wani taron tattaunawa da aka shirya domin masu neman kujerar shugaban kasa karkashin tikitin Obi/Kwankwaso a birnin Sokoto ranar Litinin.
Ya ce cin hanci da rashawa na daga cikin manyan matsalolin da ke addabar Najeriya, yana mai cewa idan aka zabe shi, gwamnatinsa za ta yaki cin hanci da rashawa a dukkan bangarorin kasar.
Obi ya bukaci ‘yan Najeriya su yi amfani da babban zaben shekarar 2027 wajen zaben ‘yan takarar NDC a dukkan matakai, yana mai cewa hakan nauyi ne na bai daya wajen magance matsalolin da kasar ke fuskanta akai-akai.






