Zan Daura In Da Tambuwal Ya Aje A Mulkin Sakkwato---Malam Ubandoma

Zan Daura In Da Tambuwal Ya Aje A Mulkin Sakkwato---Malam Ubandoma

 

Dan takarar gwamnan jihar Sakkwato a jam'iyar PDP Alhaji Sa'idu Umar Malam Ubandoma a wani martani da ya mayarwa dan takarar gwamna a APC Alhaji Ahmad Aliyu Sokoto kan kalubalantarsa da ya yi na ya fito fili ya bayyana cewa zai daura in da Ubangidansa Gwamna Aminu Waziri Tambuwal zai ajiye a mulkinsa saboda yana ganin Tambuwal ya kasa kuma ba wanda zai so hada kansa da kasawar, ya goge kalubalen in da ya furta zai daura in da Tambuwal ya ajiye.

Malam Ubandoma a jawabin da ya gabatar a gaban jama'a wurin kaddamar da yekuwar zabensa ta 2023 a ranar Laraba  ya ce zai cigaba da aiyukkan alheri da gwamnatin Tambuwal ta soma matukar ya samu nasara a zaben 2023 domin gwamnatin a tare da shi aka gudanar da ita.
Ya ce abin da za su sanya gaba shi ne "alkiblarmu daya ce ita ce jihar Sakkwato jama'a su ne gabanmu, za mu cigaba da aiyukkan alheri da Matawalle ya soma".
A jawabin gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya nemi mutane su zabi Ubandoma da Atiku da sauran 'yan takarar jam'iyar PDP daga sama har kasa don samar da maslaha a kasa baki daya.
Tambuwal ya ce sun aiwatar da aiyukkan cigaban jihar Sakkwato wadan da ake iya gani a zahiri dana boye, sauran alkawullan da suka dauka ba su iya  cikawa ba a yi hakuri sun iya kokarinsu.
Da farko babban Daraktan kamfe na PDP a Sakkwato Alhaji Yusuf Suleiman ya nemi da a zabi jam'iyar PDP ganin yanda APC ta kasa magance matsalolin tsaro da tattalin arziki har Allah ya isa ya yi ga jam'iyar.