Zamu baiwa Jonathan damar yin takara idan yana so - APC 

Uwar Jam'iyyar APC ta kasa ta bayyana cewar idan har tsohon shugaban kasa Dr. Goodluck Jonathan ya tsallako cikin Jam'iyyar to zasu sahale masa tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023 idan yana da bukatar hakan.

Babban sakataren riko na Jam'iyyar APC John Akpanudoedehe ne ya bayyana hakan a cikin shirin Politics Today da gidan Talabijin na Channels Television  ke gabatarwa game da rade radin da ake yi na komawar tsohon shugaban kasa cikin jamiyyar.
Sannan Sakataren yayi karin bayanin ceear, hakan ba yana nufin zasu bashi takara babe, za su bashi damar tsayawa domin ya kara da sauran 'yan takara da suka nuna sha'awarsu ta tsayawa Jam'iyyar a zaben 2023.
Sai dai har yanzu tsohon shugaban kasar bai ce komai ba game da batun da ake masa na sauya sheka zuwa Jam'iyyar APC mai mulki a yayin da ake fuskantar kakar zaben shekarar 2023.