Zamfara ta samu sabon kwamishinan 'yan sanda

Zamfara ta samu sabon kwamishinan 'yan sanda
 
Daga Aminu Abdullahi Gusau.
 

An tura sabon kwamishinan 'yan sanda, CP,  Ayuba Elkana, zuwa jihar Zamfara.
 
 Elkana ya maye gurbin CP Hussain Rabi'u, wanda aka sauya masa wajen  aiki don ya jagoranci rundunar ‘yan sandan Najeriya da ke jihar Imo.
 
 Sabon Kwamishinan 'yan sandan ya shiga aikin  'yan sandan Najeriya, a ranar 3 ga Maris na 1990 a matsayin Mataimakin Sufeto Janar na 'yan sanda, kuma an horar da shi a babbar Kwalejin 'yan sanda, a Kaduna.
 

 Ya yi aiki a bangarori daban daban dake cikin ma'aikatar ta 'yan sanda, wanda daya daga cikin su shi ne ya yi zama mataimakin  Kwamishinan 'yan sandan Jihar Zamfara,  mai kula da Ayyuka, har ya kai matsayin kwamishina.
 
 An tura shi hedikwatar rundunar 'yan sanda dake Abuja, a matsayin Kwamishinan 'yan sanda, (Provost Marshal,) daga baya aka sake sauya shi zuwa jihar Zamfara.
 

 Hakama sabon kwamishinan ya yi ganawa ta musamman da  kwamandojin bangarori daban daban na rundunar 'yan sanda, inda ya bukace su da su kasance masu tsare  ayyukansu, don tabbatar da da'a da halayyar kwararru, don isar da aiki  mai kyau ga jama'a.
 
 kwamishinan 'yan sanda  Ayuba Elkana, ya yi kira ga jama'a, da su inganta,  tare da dorewar hadin gwiwar da ke akwai tsakanin dukkan hukumomin tsaro, musamman, 'yan sanda, don ba su damar kawar da ayyukan 'yan ta'adda.