Zai yi wuya Nijeriya ta yi tsawon rai idan APC ta sake kafa gwamnati a 2027 - El-Eufai 

Zai yi wuya Nijeriya ta yi tsawon rai idan APC ta sake kafa gwamnati a 2027 - El-Eufai 

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa makomar Najeriya na cikin hadari idan jam’iyyar APC ta ci gaba da mulki bayan 2027.

TheCable ta rawaito cewa El-Rufai ya bayyana hakan ne a Sakkwato yayin wani gangamin wayar da kan jama'a na jam’iyyar hamayya ta hadaka, African Democratic Congress (ADC), inda ya ce yana cikin siyasa ne don ceto kasa, ba don wata riba ba.

Ya ce ya fice daga APC ne saboda gazawarta wajen tafiyar da mulki, yana mai gargadin cewa ci gaban mulkin APC zai iya rusa tubalin zamantakewa na kasar.

El-Rufai, wanda yanzu ke daya daga cikin jiga-jigan ADC, ya sha alwashin hada kai da ’yan Najeriya domin kifar da gwamnatin APC a matakin jihohi da tarayya.