Zaben Cike Gurbi:Tambuwal Na Cikin Tsaka Mai Wuya a Sakkwato

Zaben Cike Gurbi:Tambuwal Na Cikin Tsaka Mai Wuya a Sakkwato

 

Hukumar Zabe mai zaman kanta waton INEC ta saka ranar 15 ga wannan watan Assabar mai zuwa ne za ta yi dukkan zabukkan cike gurbi a kujerun majalisar tarayya da za su wakilci jihar Sakkwato da ba a kammala ba, saboda sabawa dokokin zabe.

A jihar Sakkwato ba wata kujerar dan majalisa da aka ayyana samun nasararta ciki kuwa har da biyun da suka fi daukar hankali waton wadda Gwamnan Aminu Waziri Tambuwal ke nema ta Sanata da wadda Sanata Aliyu Magatakarda ke bukatar sake komawa don wakiltar yankinsa.

A cikin kujeru uku na Sanata jam’iyar PDP ce kan gaban APC a kujera biyu in da Aminu Tambuwal ke gaban Sanata Ibrahim Danbaba dake samankujerar a yanzu  da kuri’u dubu 7,859 a yankin Sakkwato ta Kudu,  sai Honarabul Shu’aibu Gwanda Gobir ke gaban Alhaji Ibrahim Lamido da kuri’a dubu 2,059 a yankin Sakkwato ta Gabas, wanda yake saman kujerar Sanata Ibrahim Gobir bai shiga zaben ba saboda ya nemi takarar kujerar Gwamna a APC bai samu ba.

A yankin Sakkwato ta Arewa da APC ke gaba Sanata Wamakko ne gaban Mataimakin Gwamnan jiha Maniru Dan’iya da kuri’a dubu 11,732. A kujerun majalisar wakillai guda 11 APC ce kan gaba a kujeru 8 yayin da PDP ke kan gaba a kujeru 3. 

Gwamna Tambuwal a jawabinsa ga magoya bayan jam'iyar PDP a taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar satin da ya gabata bayan hukumar zabe ta sanar da faduwarsu zaben Gwamna a wani salo na dannar kirji ya  kira dan takarar gwamnansu na PDP Malam Sa'idu Umar Ubandoma  da gwamnan gobe don haka sai su gode Allah.

Ya jajantawa magoya bayansu tare da cewa mutanen Sakkwato PDP suka zaba a zaben Gwamna "amma aka ga wani abu daban ya fito a matsayin sakamakon zabe, mu musulmi ne da muka karbi kaddara wannan maras kyau a matsayin jarabawa daga mahalicci Allah, da ikon Allah za mu ci wannan jarabawa.

"Ina jawo hankalinmu kar a shige cikin gidaje ana abu kamar juyayi ko sumami don abin da ake son a samu ba a same shi a lokacin ake bukata ba, mun samu jarabawa a wannan yakin da muka fito.

"Muna sanar da ku duk matakan da yakamata a dauka na ganin abin da aka kwata ya dawo hannunmu  muna kansa, mu ci gaba da zama amintattun juna kar a zargi wani cewa wane bai yi daidai abu ne na Allah shi zai samar mana fansa, kowa yasan abin da aka yi a Sakkwato," a cewar Tambuwal.

Shugaban jam'iyar PDP Bello Aliyu Goronyo shi ma ya tofa albarkacin bakinsa na ganin ya kwantar da hankalin mutanensu ya ce sun dauki matakan da yakamata na ganin an yi nasara a kotu kan kujerar da aka kwace masu.

"akwai zaben cike gurbi inconclusive da ya rage da za a yi a 15 ga watan nan, mun dauki duk matakan da yakamata domin samun nasararmu."

Shi ma sabon Gwamnan Sakkwato Alhaji Ahmad Aliyu bayan ya karbi shedar lashe zabensa ya karawa magoya bayansa kaimi  cewa su fito su zabi APC a zaben da za a gudanar domin kara samun nasara a dukkan matakai. 

Alhaji Ahmad Aliyu Sokoto ya kara tabbatar da alkwalin da ya daukarwa mutanen jihar a lokacin yakin neman zabensa na rike jihar Sakkwato cikin adalci.

Sabon Gwamna Ahmad  ya ce ba zai ci amanar Sakkwato ba kuma ba za a hada kai da shi a ci amana ba, "zan tabbatar da samar da tsaro, da yi wa addinin musulunci aiki".

Ahmad Aliyu ya yi kira ga abokan adawa da suka yi takara tare da su zo a hada kai domin ciyar da jihar Sakkwato gaba. 

Ya kuma jajantawa mutanen PDP kan faduwa zabe da su rungumi kaddara domin Allah ne bai ba su ba, kuma shi ne ya ba mu nasara.

Masu sharhi na ganin PDP na iya sake hasarar kujerin gaba daya a zaben da za a yi ganin yanda aka samu nasara kansu a zaben gwamna wanda shi ne zabe mafi muhimmanci a jiha, da yawan magoya bayansu jikin su na iya sanyi su kasa samun karsashin jayayya da za ta kaisu da nasarar kujerun da suke kan gaba.

Haka ma wasu na ganin PDP za su fito da karfinsu domin tabbatar da nasararsu domin ba za su yarda su yi adawa ba wasu kujeru da za su iya samu domin rage zafi ba, za su fito a fafata a yi kare jini biri jini kan zaben ba tare da jin tsoro ko kula da barazanar magoya bayan APC ba.

Ana ganin Tambuwal na cikin tsaka mai wuya ne domin shi ne jagoran tafiyar PDP a jiha don haka hankalin dukkan 'yan APC na kansa da ganin an kayar da shi a kasa duk da ya ba da tazara ga abokin karawarsa.

Ana ganin Tambuwal na iya shan kasa domin mafi rinjayen rumfunan zaben magoya bayan APC sun fi karfi a wurin.

Wasu na ganin Tambuwal zai samu nasara ratar da ya bayar ba za a iya kamo shi ba don shi gwani ne ga irin wannan yakin na sunkuru da yawa sai an yarda an fi karfinsa ne ake ganin kwazo da dubarunsa a haka ne nasararsa ke tabbata.