Zaben 2023: Kuriar Mabiya Ahlulbaiti zai iya canja zaben Gwamna a Kano ---Hon. Gwarmai
Daga Ibrahim Muhammad Baba.
Gamayyar kungiyar Shi'a mai suna Ahulul Baiti United Developed Association, ta gudanar da taronta da Jami'an kananan hukumomi 44 na jihar Kano, da ya gudana a cikin Birnin Kano a jiya Asabar,
Da ya ke gabatar da Jawabinsa, shugaban Gamayyar kuma mu'assasin tafiyar, Dan Majalisar Jihar Kano mai wakiltar kananan hukumomin Kunchi da Tsanyawa, Hon. Garba Ya'u Gwarmai ya jaddada cewa siyasa adadin mutane suke nema,
"Don haka Ina tabbatar maku da cewa kuriar 'yan shia a jihar Kano sunfi Miliyan 1 don haka duk wanda muka marawa baya sh ne zai samu nasara"
Sannan ya yi kira ga membobin wannan hadaka da su yi aiki tukuri don ganin tafiyar ta yi nasara.
Tun da farko a Jawabinsa, Hon. Adamu Kabir Auduwa, wanda shi ne shugaban Gamayyar na jiha ya ce babbar manufar tafiyar shi ne a hada kan mabiya Ahlulbaiti a duk inda suke a siyasance,
Inda ya ce "mun hadu ne don zama a tattauna a Samarwa da yan wannan mazhabin na Ahlulbaiti mafita da zai sa mu samu yanci na addinmu, walwalarmu da kuma duk wasu hakkoki da yan kasa suke amfana mu ma mu amfana".
Taron dai ya samu halartar shugabanni Gamayyar kungiyar na kasa da na jiha da ma wasu kungiyoyi da suke da alaka da su.
managarciya