Za'a  Shawo Kan Matsalar Sabbin Kudi Nan Da Kwana 7----Buhari

Za'a  Shawo Kan Matsalar Sabbin Kudi Nan Da Kwana 7----Buhari

 

Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci 'yan Najeriya da su bashi kwanaki bakwai kacal domin ya shawo kan matsalolin da suka kawo karancin sabbin takardun kudi. 

Kamar yadda ya jaridar The Cable ta wallafa, Shugaban kasan yace ya ga rahotanni da ke nuna karanci da kuma illar da rashin kudin ya janyowa kasuwanci da jama'a talakawa. 
Yace ragowar kwanaki bakwai daga cikin goma da aka kara kan wa'adin amfani da sabbin kudin za a yi su ne ana shawo kan matsalolin da suka hana nasarar tabbatar da tsarikan sabbin kudin. "Zan koma kan babban bankin Najeriya da kamfanin buga kudi. 
Za a yanke hukunci a cikin ragowar kwanaki bakwan nan da aka kara." 
Ya bayyana matsayarsa ne yayin da ya gana da gwamnonin Najeriya da ke karkashin inuwar jam'iyya mai mulki ta APC. 
Sannan a wallafar da shugaban kasan yayi a shafinsa na Twitter, yace ya san halin matsain da 'yan Najeriya suka shiga sakamakon musayar takardun kudin. 
Matsalar dai rashin tsabar kudi na cigaba da kamari a cikin gari wanda lamarin ke durkusar da san'ao'i masu tarin yawa a Najeriya.