Zaɓen ƙananan hukumomi: Gwamnatin Kebbi ta gargaɗi PDP

Zaɓen ƙananan hukumomi: Gwamnatin Kebbi ta gargaɗi PDP
 
Gwamnatin jihar Kebbi ta yi kira ga jam'iyar adawa a jihar PDP ta daina fadin abin da mataimakin Gwamnan jihar Sanata Umar Abubakar Tafida bai fadi ba, kan zaben kananan hukumomin jihar da za a gudanar a watan Agustan wannan shekara.
Sakataren kafafen yada labarai na gwamnatin jihar Kebbi  Alhaji Ahmad Idiris ya fitar da bayanin martani ga sakataren PDP na jiha Abubakar Bawa Kalgo kan ya fadi abin da mataimakin gwamna bai fada ba.
Idiris ya ce ba wani wuri da aka furta cewa gwamnatin APC ta kammala kowane shiri na cin zaben kanannan hukumomi  da karfi a jiha.
"Ina son nasar da PDP a jihar Kebbi abin da mataimakin gwamna ke nufi a kalamansa, shi ne yanda Gwamnan jiha Kwamared Nasir Idiris ya yi aiyukka masu kyau ga mutane, mun san APC ba ta da wata matsala a zaben kananan hukumomi dake zuwa.
"Ina son PDP ta sani kar ta bari tsoron da ta shiga ya sa ta rika suka marar ma'ana, zaben zai kasance sahihi mai inganci," a cewarsa.
Ya ce ba su ce mutane za su zabi APC da karfi ba, amma dai mutane za su zabe su saboda abin da gwamnati ta yi masu a kananan hukumomi 21.
Ya ba da tabbacin zaben zai zama na gaskiya da adalci kan haka ba wani dalili da zai sa wata jam'iyar adawa ta sanyawa kanta tsoro.