Yunƙurin IBB Zai Taimakawa Matasa Masu Tasowa-----Gwamnan Ekiti

Yunƙurin IBB Zai Taimakawa Matasa Masu Tasowa-----Gwamnan Ekiti

Yunƙurin IBB Zai Taimakawa Matasa Masu Tasowa-----Gwamnan Ekiti


Gwamnan jihar Ekiti kuma shugaban gwamnonin Najeriya, Dakta Kayode Fayemi ya bayyana cewar qoqari da yunkurin tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida abu da ke nuni cewar dan matasa masu tasowa yake yin sa.
Dakta Fayemi ya bayyana hakan ne a lokacin da ya samu rakiyar gwamnan jihar Kebbi kuma shugaban kungiyar gwamnonin jam'iyyar APC, Abubakar Atiku Bagudu a madadin sauran gwamnonin kasar nan dan ziyartar tsohon shugaban kasar Janar Babangida a gidansa da ke Hilltop a cikin garin Minna fadar gwamnatin jihar Neja dan taya murnar cika shekaru tamanin da haihuwa.
Shugaban gwamnonin Najeriyar yace, Janar Babangida ya cancanci yabo saboda irin gudunmawar wajen cigaban kasar nan, ta hanyar tabbatar da hadin kan kasa a lokacin yana mulkin kasar cikin kakin soja, ya kara da cewar ziyartar ta mutuntawa ne kan gudunmawar da mulkinsa ya bayar ga qasar nan.
" Yace ya kamata a kira shi da soja mai kwazo, kwararre wajen hadin kan al'ummar kasa, wanda ya jagoranci kasar da gaskiya.
Yayi abubuwa da dama dan ceto kasar nan bisa kwazo da jajircewa, ya samar da cigaba sosai a kasar nan".
Dakta Fayemi, yace wanda ya assasa cigaban kasar tabbas cigaban zai cigaba da wanzuwa, yace babu shugabancin da zai samu kalubalen da za a iya tafiyarwa, face kalubalen ya zama tarihi.
Shugaban gwamnonin, yayi addu'ar samun lafiya da kwarin guiwa da ilimin cigaba da bada shawarwari na gari ga matasa masu tasowa akan kwarewarsa dan samun al'umma ta gari mai inganci.
Gwamna Abubakar Sani Bello ne ya jagoranci yan uwansa gwamnonin zuwa gidan tsohon shugaban kasar Janar Ibrahim Babangida a Hilltop.
Gwamnonin sun ziyarci tsohon shugaban kasa Janar Abdussalam Abubakar a gidansa.