YOSEMA ta sha alwashin tallafin N1.4bn ya shiga hannun wadanda abin ya shafa 

YOSEMA ta sha alwashin tallafin N1.4bn ya shiga hannun wadanda abin ya shafa 

Daga Muhammad Maitela, Damaturu.

Shugaban Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa na jihar Yobe, Dr. Muhammad Goje ya sha alwashin raba tallafin Naira Biliyan 1.4 wanda Gwamnatin jihar ta ware domin wadanda ibtila'in ambaliyar ruwa ya shafa a jihar, wajen yin adalci da rikon amana; ba tare da la'akari da bambanci ko bangare ba a fadin jihar.

Wannan bayanin ya fito ne daga bakin Babban Sakataren Hukumar SEMA, Dr. Mohammed Goje, a ranar Litinin a sa'ilin da yake zantawa da manema labaru a gidan Gwamnatin jihar dake Damaturu, tare da nanata cewa hukumar za ta yi dukkan abin da ya dace don ganin tallafin ya shiga hannun wadanda aka tsara tallafin domin su. 

Har wala yau kuma ya bayyana jin-dadinsa dangane da ingantattun tsare-tsaren da ake dasu a kasa na rarraba tallafin kudaden da gwamnatin jihar ta samar ta hanyar hada kai da shugabannin al'umma, kungiyoyin mata da wakilan matasa. 

Dr. Goje ya kara da cewa gwamnatin Mai Mala Buni za ta ci gaba da zage damtse wajen ganin ta shawo kan matsalolin bala’in ambaliyar ruwa a fadin jihar Yobe, ta fannin samar da shirye-shirye na dogon zango, matsakaici da gajeren zangon dakile matsalolin baki daya. 

Ya bayyana cewa wannan shiri na bayar da tallafin makudan kudade ya na daga cikin kokarin da Gwamnatin Gwamna Buni take yi wajen rage wahalhalun da ambaliyar ruwa ga masu karamin karfi a fadin jihar.

“Kamar yadda Gwamna Buni ya ba da umarni, Hukumar SEMA ta dukufa wajen raba kayan abinci, na masarufi, tare da sauran kayan suka shafi bukatun yau da kullun matsayin tallafi ga wadanda ambaliyar ruwan ta shafa da kuma marasa galihu. 

“Raba wannan tallafin kudaden zai zo ne bayan samar da ingantaccen tsari da hukumar SEMA za ta gudanar ta hanyar hada karfi da karfe tareda al’umma, kwamitin tuntuba da tantancewa kan Ambaliyar ruwa, da sauran jami’an gwamnati.

“Haka zalika kuma, wannan tallafin kudaden, na musamman ne kuma wani bangare ne na dabarun daukar matakan da suka dace nan-take don rage radadin ambaliyar ruwan, wanda Maigirma Gwamna Buni, duk da a baya ya sha daukar irin wadannan matakan tallafawa al'ummar da irin wannan ibtila'in ya shafa a baya.

“Tallafin kudaden hadi da ci gaba da rabon kayayyakin abinci, kayan masarufi, kayan gini, da na tsafta, ya kara nuna kyakkyawan kudirin wannan gwamnati na samar da cikakkiyar kulawa ga muhimman bukatun al'ummar ta.

Sakataren Hukumar Bayar da Agajin Gaggawar ya ce SEMA za ta ci gaba da mayar da hankali wajen ganin an shawo kan kalubalen ibtila'in ambaliyar ruwan, tare da yin aiki tukuru wajen ganin ta cimma ingantattun manufofin Gwamna Buni wajen farantawa wadanda al'amarin ya shafa a fadin Jihar Yobe.