Yobe ta dage dokar hana hawa babur mai kafa biyu a kananan hukumomi 7

Daga Muhammad Maitela, Damaturu.
Gwamnatin jihar Yobe ta dage dokar hana hawa babura masu kata biyu a Yobe ta Gabas, yankin da ya kunshi kananan hukumomi bakwai a jihar Yobe, da ranar yau Litinin.
A sanarwar manema labarai wanda ofishin mataimaki na musamman ga Gwamna kan harkokin tsaro ya fitar, Brigadier General Dahiru Abdulsalam (Mai ritaya) inda ya kara da cewa, Gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni shi ne ya amince da dage haramcin.
Ya kara da cewa, "An dage wannan haramci na hawa babur mai taya biyu, daga yau 6 ga watan Maris 2023 a cikin kananan hukumomi 7 dake Yobe ta Gabas (Zone A) da suka kunshi: Bursari, Damaturu, Geidam, Gujba, Gulani, Tarmuwa da Yunusari."
Haka kuma sanarwar ta ce an dage haramcin bisa ga sharuddan, "Baburan za su rinka aiki ne daga 6:00 na safe zuwa 6:00 na yamma a kowace rana. Sannan ba a lamunta ayi haya ko Achaba da su ba. Kana kuma mutum daya aka yarda ya hau ba tare da goyo ba."
"Har wala yau kuma, dole duk masu mashin su yi rijista tare da yankar lasisi da sauran kaidojin mallaka a karamar hukumar da mai mashin din yake ga hukumar kula da ababen hawa ta jihar Yobe (YOROTA) da hukumar bayar da lasisi ta jihar baki daya. Sannan dole kowane mai babur ya tsaya iya karamar hukumar da yake."
Bugu da kari, sanarwar ta bayyana cewa, "Idan aka kama mai tuka babur ya dauki fasinja, za a hukunta shi kamar yadda doka ta tanada. Sannan kuma ba a yarda ayi zirga-zirga da babura daga wannan karamar hukuma zuwa wacan ba, yin hakan saba doka ne."
A karshe, Dahiru Abdussalam ya bayyana cewa, "dukan jami'an tsaro za su sanya ido domin tabbacin jama'a sun bi doka dau da kafa."