Yayin gabatar da kasafin kuɗi, Tinubu ya faɗawa ƴan majalisa cewa duk za su lashe zaɓen su a 2027

Yayin gabatar da kasafin kuɗi, Tinubu ya faɗawa ƴan majalisa cewa duk za su lashe zaɓen su a 2027

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a ranar Laraba ya yi barkwanci inda ya ce ‘yan majalisar dattawa ta 10 sun “sake cin zaɓe.”

VANGUARD ta rawaito cewa hakan ya faru ne lokacin da shugaban ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2025 ga taron hadin gwiwa na Majalisar Dokoki ta Ƙasa.

Tinubu ya yi wannan furuci ne bayan ya yi kuskure wajen kiran majalisar dattawa ta 10 da sunan ta 11.

Ya yi wannan barkwanci ne bayan wasu daga cikin ‘yan majalisar sun gyara shi, kamar yadda aka gani a wani bidiyo da ya bazu wanda ke da tsawon minti ɗaya da dakika 14.

"Domin cika ɗaya daga cikin hakkokina na doka tare da jajircewa wajen sake gina Najeriya da tabbatar da mun tsaya tsayin daka a tafiya mai zuwa ta samar da makoma mai albarka, na gabatar da kasafin kudin 2025 ga taron hadin gwiwa na Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta 11,” in ji Tinubu.

Bayan wannan, ‘yan majalisar sun tuna wa Shugaban cewa su ne Majalisar Dokoki ta 10.

“Ta 10? Na rubuta ta 11, wanda ke nufin kun sake cin zaɓe gaba ɗaya,” Shugaban ya amsa da dariya.