Yaushe Ne Danfulani Zai Biya Managarciya Bashin Da Take Binsa?

Yaushe Ne Danfulani Zai Biya Managarciya Bashin Da Take Binsa?

Dan siyasa a jihar Sakkwato mai neman tsayawa takarar dan majalisar tarayya a kananan hukumomin Sakkwato ta kudu da Arewa Honarabul Sanusi Danfulani Mujallar Managarciya ta yi masa aiki na musamman tun a watan 9  a shekarar 2020  yake yi wa kamfanin je ka dawo har zuwa yanzu da kake karanta rubutun nan bai biya hakkin kamfani ba.

Kamfanin DMM Media and Services LTD, ya yanke shawarar   gabatar da wasu rubutu  guda biyar da suka shafi wannan dan siyasar, kan harkokin siyasarsa da mu’amala da mutane a matsayin tukuici ga abin da ya yi wa kamfani, abin da zai zama fitila da za ta haska wa mutane domin su rungumi dan siyasar ko a ajiye shi wannan shawara ta rage ga wanda zai karanta rubutun da zai zo bayan wannan.

Managarciya Mujalla ce da ake bugawa a jihar Sakkwato da ta shafi dukkan bangarorin rayuwa na yau da kullum, takan fitar da bugu na musamman kan wani ko wasu mutane da ta gamsu da mutunci da kimarsu a idon al’umma.

Kamfanin Mujallar Managarciya ba a kafa shi domin ya yafe hakkinsa da ke hannun kowa ba, sai dai in aka rike hakkinsa zai yi magana a kafarsa kuma ya biyo da tukuicin rubutu domin ya taimaki al’umma kar su fada a homar da ya fada.

Mu hadu da kai a kashi na daya a rubutunmu mai taken ‘WANE NE HONARABUL SANUSI DANFULANi?’