INGREDIENTS
Flour 2 cup
4 Eggs
Melted butter/ oil
Pinch of salt
Baking powder 2teaspoon
Mango juice (I used mango Gofresh drink) 1/4 cup ×2
Powdered suger
Yellow food colour
Flavor
PROCEDURE
Ki fara fasa ƙwayayenki a cikin mazubi mai tsafta sai ki saka powdered sugar ki yi whisking sosai (ni dai na yi blending ne) har sai kalarsa ta zama fari.
Daga nan sai ki ɗauko fulawarki ki saka baking powder a kai ki yi whisking sai ki dinga zuba ta a cikin wet ingredients ɗin a hankali kina juyawa, ki sake zubawa har dai ki juye duka (bit by bit zaki dinga zuba fulawar ba bai ɗaya ba saboda kar ta yi gudaji)
Sai ki zuba melted butter or oil ki juya, sannan ki saka yellow food colour kaɗan sai ki zuba mango juice ɗinki a kai ki juya a hankali (don't over mix)
idan kika tabbatar ya haɗe jikinsa sai ki yi greasing pan ɗinki ki shafa butter ki barbaɗa flour sannan ki shimfiɗa baking paper a kai sai ki juye batter ɗin a ciki ki gasa da wutar sama da ƙasa (Ni dai ba da oven na yi nawa ba)
Wani albishir a gare ki, ba lallai sai kina da oven ba ko kuma kin jira Nepa ba. Daga lokacin da kika gama kwabinki zaki iya ɗora tukunyarki a kan wuta ki zuba ruwa kaɗan a ciki sai ki danne ruwan da wani murfi da zai shiga cikin tukunyar, idan ruwan ya fara zafi sai ki ɗauko pan ɗinki ki ɗora ta a kan wannan murfin sai ki saka babban murfi na tukunyar ki rufe (kamar dai zaki yi alale) sai ki ba shi kamar 20 minutes sai ki duba, ki saka tsinke a jikin cake ɗin, idan kika fito da shi ba kulli a jiki to cake ɗinki ya zama ready sai ki sauke.
Enjoy it
Don't forget to share
RUKY'S BAKERY