'Yan Ta'adda Sun Kai Wa Mataimakin Sifeto-Janar Na 'Yan Sanda Hari
Wasu ƴan ta’adda sun kai farmaki kan ayarin motocin Mataimakin Sifeto-Janar, AIG na ƴan sanda na shiyya ta 12 da Shelkwatar sa ke Bauchi, Audu Madaki, inda suka raunata shi tare da kashe ɗaya daga cikin dogaransa.
Rahotanni sun bayyana cewa AIG din na kan hanyarsa ne ta zuwa Abuja daga Bauchi lokacin da wasu da ake zargin ƴan ta'adda ne suka yi wa motarsa kwanton-ɓauna.
Rahotanni sun yi nuni da cewa lamarin ya faru ne a tsakanin Barde da Jagindi a Jihar Kaduna a jiya Talata da misalin karfe 2:30 na rana.
Rahotanni sun ƙara da cewa AIG din yana karbar magani a wani asibiti da ba a bayyana ba yayin da aka tsaurara matakan tsaro a kewayen shiyyar.
managarciya