'Yan Sandan Sun Kama Masu Garkuwa da Mutane Yayin Karɓar kuɗin Fansa a Gombe
Daga Rabilu Abubakar, Gombe.
A kokarin rundunar Yan Sandan Jihar Gombe na kawar da ayyukan ta'addanci a fadin jihar, rundunar ta yi nasarar kama wasu mutum 2 da ake zargin masu Garkuwa da Mutane ne masu suna Mohammed Aminu da Salisu Sa’idu da dukan su suke zaune a unguwar Tudun Wada a fadar jihar.
Batun hakan yana dauke ne a wata takarda mai dauke da sanya hannun Jami'in hulda da Jama'a na hukumar ASP Mahid Mu'azu Abubakar, a madadin Kwamishinan Yan Sanda Ishola Babatunda Baba'ita da aka rabawa manema labarai.
Yace an kama wadanda ake zargin masu Garkuwa da mutanen ne a lokacin da suke kokarin karbar kudin fansa na naira dubu dari uku bayan yan uwan wanda suka kama din sun biya naira dubu dari tun farko.
Mahid Abubakar, yace a lokacin da suke tuhumar wadanda ake zargin Sa'idu Salisu ya bayyana musu cewa sun samu bindiga kirar AK 47 guda 3 ne suka je suka dauki wani mai suna Jibrin Muhammad dake kauyen Bantaje a jihar Taraba, suka yi Garkuwa da shi har suka karbi kudin fansa naira miliyan hudu.
A cewar yan sanda a binciken da suke yi ne suka yi nasarar kama Salisu Sa'idu, a jihar Kano wanda jami'an Yan sandan farin kaya na SCID na Gombe suka kama, yanzu haka kuma suna ci gaba da bincike da zarar sun kammala za su tura su zuwa Kotu.
Daga nan sai Kwamishinan yan sandan Ishola Babatunde Baba'ita, ya kirayi al'umma da cewa su ci gaba da basu hadin kai wajen sanar da su rahoton abubuwan dake faruwa a yankunan su da sanar da duk wani motsi ko zirga-zirgan wasu da basu yarda da su ba ga hukumomi dan daukar mataki
managarciya