Rundunar ‘yan sandan jihar Sakkwato ta yi nasarar lalata shirin ‘yan bindiga in da suka ƙwato dabbobin da suka sata a ƙauyen Anada cikin ƙaramar hukumar Binji.
A ranar Alhamis aka kira jam’i’an ‘yan sanda aka sanar da su ‘yan bindiga masu yawa sun kai farmaki ƙauyen Anada sun riƙa harbi kan mai uwa da wabi a yankin har sun sace dabbobi 43 na mutanen gari.
Ba da wasa ba nan take jami’an ‘yan sanda suka tashi tawaga suka datse hanyar fita garin bayan musayar wuta ta ɗan lokaci, ‘yan bindigar suka bar dabbobin suka shiga daji na kusa da garin.
A bayanin da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar DSP Ahmad Rufa’i ya fitar ya ce an ƙwato Tumakai 43 dukansu da aka sace.
“Muna kira ga mutane su sanar da duk wani mutum da suka gani da miki a yankin don ganin jami’an mu da ke wurin sun ɗauki matakin da yakamata.
“Kwamishinan ‘yan sanda na Sakkwato CP Hayatu Hassan ya yabawa babban jami’in ‘yan sanda dake kula da ƙaramar hukumar Binji yanda shi da jami’an sa suka nuna ƙwarewa da ƙwazo kan kare rayuwa da dukiyar mutane. Ya kira gare da su ci gaba da samar da bayanan sirri domin cigaba da taimakon ‘yan sanda a wurin kare rayuwar mutane.





