'Yan Sanda sun kama mutane 81 Kan Zanga-zanga a Sakkwato

'Yan Sanda sun kama mutane 81 Kan Zanga-zanga a Sakkwato
 
Rundunar 'yan sandan jihar Sakkwato ta fitar da sanarwar kama matasa mutum 81 da suka sabawa doka a lokacin gudanar da zanga-zanga a ranar farko kamar yadda kwamishinan 'yan sanda na jiha Ali Hayatu ya sanar  ya ce za su cigaba da baiwa mutanen jiha tsaro a lokacin da ake gudanar da zanga-zangar.
A bayanin da jami'in hulda da jama'a na 'yan sandan ASP Ahmad Rufa'i ya fiyar ya ce Kwamishina ya jinjinawa dukan jami'an tsaron jiha kan hadin kan da aka samu na aiki tare wanda hakan ya sanya samun nasarar kama matasa 81 da suka saba doka.
Ya ce matsa sun yi zanga-zanga cikin lumana har zuwa bayan Azahar da lamarin ya sauya wasu suka farwa kayan gwamnati domin barnatarwa.
Ya ce daga nan ne jami'an tsaro suka yi kokari na dawo da bin doka don kaucewa farfasa shagunan mutane a birnin jiha.
An gudanar da zanga-zangar lumana a kananan hukumomin Isa da Goronyo ba tare da samu wata hatsaniya ba.
Kwamishina ya ce jama'a na da damar su yi zanga-zangar lumana, amma duk wanda ya yi amfani da damar ya barnata kayan gwamnati ko kawo tashin hankali hukuma za ta kama shi domin a hukunta shi.