'Yan sanda sun kama dan bindigar Lukurawa da shanu 10 a Kebbi

'Yan sanda sun kama dan bindigar Lukurawa da shanu 10 a Kebbi
Rundunar 'yan sanda jihar Kebbi sun yi nasarar kama dan bindigar Lukurawa daya da shanu 10 a wani samame da suka kai a kasuwar shanu dake garin Bachaka.
Jami'in hulda da jama'a na 'yan sandan Kebbi CSP Nafi'u Abubakar a bayanin da ya fitar ya ce "a ranar Lahadi data gabata a bayanan sirri da muka samu cewa wani Salihu Umar mai shekaru 42, dan haifar garin Dogon Dutse dake Jamhuriyar Nijar ya shigo kasuwar shanu ta Bachaka tare da shanu 10 da ya sacewa Usman Aliyu na garin Zogirma a karamar hukumar Bunza a Kebbi."
Ya ce suna cikin shanu 68 da ake zargin  Lukurawa sun sace a ranar 20 ga watan Agusta suka tsallaka Nijar da su.
"Kwamishinan 'yan sanda CP Bello M Sani ya jinjinawa sashen bayanan  sirri na DPOn Bachaka da mutanensa, kan wannan nasarar da suka samu ya kuma nemi su kara matsa kaimi kan kariyar al'umma."
Kwamishina ya kudurci kara kokari don ganin an kama sauran mambobin tare da kwato sauran shanun da aka sace.
Ya ce CP Bello Sani ya saudakar da kansa don ganin ya tabbatar da ɓatagari da ba su son zaman lafiya ba su yi nasara ba, ya yi kira ga masu son zaman lafiya da su zama a fadake da ba da goyon baya ga 'yan sanda da sauran jami'an tsaro, wurin bayar da bayani kan lokaci don daukar matakin da ya dace.