'Yan sanda sun fatattaki Boko Haram, sun dakile wani harin bam a Borno

'Yan sanda sun fatattaki Boko Haram, sun dakile wani harin bam a Borno
 
 
Rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta yi nasarar dakile wani hari da ‘yan Boko Haram suka kai tare da tarwatsa wani bam da aka dasa a kauyen Malari da ke karamar hukumar Konduga a ranar Laraba.
 
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Nahum Daso, ya fitar, ya ce harin ya faru ne da misalin karfe 1:00 na safe, lokacin da mayakan Boko Haram/ISWAP suka kai farmaki a sansanin ‘yan gudun hijira na Forward Operating Base (FOB) da ke Malari.
 
Daga Abbakar Aleeyu Anache