'Yan sanda sun cafke ɗan shekara 84 ya yi wa ƴar shekara 8 fyade

'Yan sanda sun cafke ɗan shekara 84 ya yi wa ƴar shekara 8 fyade

Yan sanda a Ogun sun kama wani dattijo mai shekaru 84, Stephen Jack, da laifin yi wa ƴar shekara takwas fyaɗe.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ya bayyana haka a Abeokuta s yau Asabar, inda ya ce wanda ake zargin yana zaune ne a unguwar Okun Owa da ke Ijebu-Ode, kuma ya yi ƙaurin suna a neman ƙananan yara.

Ya ƙara da cewa mahaifin wanda aka kashen ne ya kai rahoton kubucewar Jack ga ‘yan sanda da ya lura cewa ‘yarsa na zubar da jini daga yankinta.

Oyeyemi, Sufeto na ƴan sanda, ya bayyana cewa da aka yi masa tambayoyi, wacce a ka yi wa fyaɗen ta shaida wa mahaifinta cewa Jack ya yi lalata da ita.

Ya kara da cewa an kai yarinyar  zuwa babban asibitin Ijebu-Ode domin yi mata magani.

Kwamishinan ƴan sanda a jihar, Lanre Bankole, ya kuma bayar da umarnin a kai Jack sashen binciken manyan laifuka domin gudanar da bincike tare da gurfanar da shi gaban kuliya.