Home Siyasa ‘Yan Nijeriya ne za su ɗauki nauyin kamfen jam’iyarmu—NDC

‘Yan Nijeriya ne za su ɗauki nauyin kamfen jam’iyarmu—NDC

18
0

Jam’iyyar NDC na so talakawan Nijeriya su ɗauki nauyin kuɗaɗen gangamin yaƙin neman zaɓen ta

Jam’iyyar NDC ta ce tana shirin fara tara kuɗaɗen gudanar da yaƙin neman zaɓenta na 2027 ta hanyar gudummawar kuɗi daga talakawan Nijeriya, maimakon dogaro da attajirai da masu bayar da kuɗaɗen siyasa.

Jam’iyyar ta ce za a bai wa ƴan Nijeriya damar bayar da gudummawar kuɗi daga naira 1,000 ko 2,000 zuwa sama domin tallafa wa yaƙin neman zaɓenta.

Ta bayyana tsarin a matsayin wani yunƙuri na rage tasirin masu hannu da shuni a kan tsarin dimokuraɗiyyar ƙasar.

Shugaban jam’iyyar na ƙasa kuma Sanata mai wakiltar Bayelsa ta Yamma, Seriake Dickson, ne ya bayyana hakan yayin wata hira da shirin Prime Time na gidan talabijin na Arise News.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here