'Yan Majalisa Sun Fara Shirin Tsige Mataimakin Gwamnan Zamfara

'Yan Majalisa Sun Fara Shirin Tsige Mataimakin Gwamnan Zamfara

‘Yan majalisar Jihar Zamfara sun fara shirye-shiryen tsige mataimakin gwamnan jihar Mahadi Aliyu Gusau a wani sabon yunkuri da suka soma bayan na baya ya sha kasa.

 Mataimakin kakakin majalisa ya gabatar da  takardar tsigewa ga shugaban majalisa.

   Mataimakin kakakin majalisar, Musa Bawa ya hannunta takardar ga   kakakin majalisar, Nasiru Mu’azu Magarya a ranar Juma’a a Gusau, babban birnin jihar. 

An samu bayanai dangane da yadda majalisar ta zargi mataimakin gwamnan da yin karantsaye ga kundin tsarin mulkin jihar da kuma amfani da matsayinsa wurin yin sama da fadi. 
Sai dai ba a san dalilin mataimakin kakakin majalisar ba, wanda ya sanya  shugabancin kwamitin asusun gwamnati  na daukar wannan matakin.
Dangantaka ta yi tsami a tsakanin Gwamna da mataimakinsa tun bayan da Gwamna Berllo Matawalle ya koma jam'iyar APC in da mataimakin gwamna ya ce shi ba zai koma ba.