'Yan Bindiga Suna Karɓar Shinkafa da taliya matsayin Kudin Fansa domin yunwa ta kama su a daji
Sakamakon matsin lamba da gwamnatin jihar Zamfara ke ma 'yan ta'addan jihar, maimakon su nemi kuɗin fansa sun koma buƙatar buhunan shinkafa, kwalayen taliya da ruwan lemon roba da gwangwani.
'Yan Bindiga Suna Karɓar Shinkafa da taliya matsayin Kudin Fansa domin yunwa ta kama su a daji
'Yan Bindigar Zamfara sun fara shiga mawuyacin hali na rashin abinci inda suka fara buƙatar buhunan shinkafa da kwalayen taliya a matsayin kuɗin fansa.
Sakamakon matsin lamba da gwamnatin jihar Zamfara ke ma 'yan ta'addan jihar, maimakon su nemi kuɗin fansa sun koma buƙatar buhunan shinkafa, kwalayen taliya da ruwan lemon roba da gwangwani.
Wasu mazauna yankin sun sanar da yadda yunwa ta gigita yan bindiga har suka karbi mudu goma na shinkafa a matsayin fansa.
Wani mazaunin Sabon Birni, wanda ya bukaci a rufa sunan shi, ya sanar da Daily Trust yadda aka sako wata ɗiyar makwabtansu bayan sun ba da kayan abinci.
Mutumin ya ce; “Sun sace ɗiyar wani mutum a ƙauyenmu kuma ya kasa haɗa kuɗin fansa sai suka ce ya kai mudu goma na shinkafa a matsayin fansar ɗiyarsa”.
managarciya