Ina So A Riƙa Tunawa Da Ni A Matsyin wanda Ya Gyara Najeriya----- Buhari
Akan zabukan 2023 dake tafe nan gaba, Shugaban ya ƙara Jaddada zagewar sa kan anyi Zaben cikin lumana da adalci, ya bukaci shugabanin dasu wayar da kan mutanen su ta hanyar data dace kan bukatar su tuntubi wakilan su da suka zabe su hakkokin su.
Ina So A Riƙa Tunawa Da Ni A Matsyin wanda Ya Gyara Najeriya----- Buhari
Shugaba Muhammad ya ce yana so a rika tuna wa da shi a matsayin wanda ya daidaita Najeriya ta fuskar tsaro da tattalin arziki da habbakar kasa da nasarar da ya samu wajen yaki da cin hanci da rashawa.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Femi Adesina ya fitar ya ce Buhari ya bayyana hakan ne a Owerri Babban Birnin Jihar Imo
Shugaban ya bayyana wa shugabannin kudu maso gabashin Najeriya a wata ziyara da ya kai ta kwana guda a jihar Imo cewa, cikin abin da ya yi kasa da shekara biyu da ya rage na mulkinsa, har yanzu harkar tsaro ita ce abin da ya fi bayar da hankali kansa.
"Matukar babu tsaro, ba wani abu da wani zai iya yi komi irin kintsawa da yayi.
"Tsaro shine ginshikin abu na farko Sa'annan sai tattalin arziki. Da zarar mutane sun samu tsaro zasu maida hankali kan kasuwancin su," inji shugaban.
"Babu wanda zai iya zargina da cewa na mallaki Kamfani ko Katafaren gida a kowane guri a Ƙasar, kuma na godewa Allah ina ta kokarin kamanta kan abinda zai yiwu, ta yadda ba za'a samen da aikata ba daidai ba.
"Zanyi dukkan iyawa ta don tabbatar da cewa Ƴan-Nijeriya da suke kokari Tukuru, sunyi nasara kan yunkurin su," Cewar Shugaban.
Akan zabukan 2023 dake tafe nan gaba, Shugaban ya ƙara Jaddada zagewar sa kan anyi Zaben cikin lumana da adalci, ya bukaci shugabanin dasu wayar da kan mutanen su ta hanyar data dace kan bukatar su tuntubi wakilan su da suka zabe su hakkokin su.
Da yake yabo kan irin arziki da kasuwanci irin na Ƴan kabilar Ibo, shugaban yace;
Abu mafi Muhimmancin ga Ƴan kabilar Ibo Shine, babu wani gari dazaka ziyarta a Najeriya ba tare da ganin Dan kabilar Ibo wa lau jagora akan abun more rayuwa ko kamfanin samar da magani.
"A saboda haka, abinda mamaki ne gare ni cewa Dan Kabilar Ibo ya dauki kanshi cewa shi ba wani sashe na Najeriya ne ba.
"Hujjoji na Nan fa kowa don su gani cewa Dan kabilar Ibo suke Manyan jagorori a tattalin arzikin Najeriya."
Ya nunar cewa, babu wata kasa da zata samu wani cigaban azo a gani ba tare da da samun cigaban Manyan aiyukan gina ƙasa ba, Shugaban kasar ya bayyana na damar sa, cewa Gwamnatocin daya gada a matakin tarayya sun taka rawa Gurin koma bayan shimfida Manyan aiyuka a Ƙasar.
Yayi Alkawari cewa, Gwamnatin Tarayya zata kammala aiyukan da take aikatawa a yankin Kudu maso Gabas, ciki harda Babbar Gada na (2nd Niger Bridge) dama kuma layin dogo daya kara de da hada Shiyar da Sauran sassan Kasar.
"Ina da karfin imnai cewa, idan aka samu aiyukan Cigaba daya dace, Ƴan-Nijeriya zasu maida hankali wajen kasuwancin su," inji shi. Ya kara da cewa a Matsayin kungiyar, Ƴan kabilar Ibo zasu ci Moriya sosai daga aiyukan Cigaba da ake aikin su a Ƙasar, saboda" sune kan gaba Gurin kasuwanci."
Shugaba Buhari tun da farko, ya bude aiyuka guda Hudu wanda Gwamnan jihar Imo Hope Uzodinma yayi su, ciki harda hanyar data hada Naze/Ihiagwa/Nekede/Obinze da aikin ma gudanar ruwa ta Balloon Driven/Flood Control drainage a hanyar da ake cewa Tiger, da hanyar baya ta sabon Exco-Chambers a gidan Gwamnati dake Owerri.
Da yake jawabi ga mazauna Gurin a yayin bude aiki hanyar baya ta Egbeada bypass, wanda aka sanya sunan Sananne kuma Muhimmin Dan Jihar, Cif Emmanuel Iwuanyanwu, Shugaban kasa yace, ya gamsu sosai kan mataki da aiki ya kai wanda Gwamnatin jihar tayi.
"Nayi murna sosai da abinda na gani da ido na, Ina baku tabbaci cewa zan Tallafawa jihar Imo dai dai da yadda dokar Gwamnatin Tarayya Najeriya ta tanadar," inji shi.
Cikin jawabin sa, a Gurin taron, Gwamnan Jihar Uzodinma, yace Ƴan kabilar Ibo sun amince da gamsuwa da hadin kan Najeriya, kan Adalci, daidaito."
Gwaman ya godewa Shugaban kasa, bisa inda yake biyan bukatun Al'ummar Ibo ta hanyar Samar da tsari da shirye shirye da aka Samar don bawa mutane kulawa ta gaskiya, ciki harda aikin gina babbar gada ta 2nd Niger Bridge, da Sauran su.
Gwamna Uzodinma, yace Al'umman Yankin Kudu maso gabashi sun kasance masu Godiya ga Shugaban Kasa, dangane da amincewa da kafa Barikin Sojin Ruwa a yankin karamar Hukumar Oguta na jihar, ya kara da cewa nan gaba, alfanun sa ga tattalin arziki zai bayyana.
Gwamnan. Ya kuma yabawa Shugaban kasa, bisa nuna goyon baya don bada Muhimman Mutane Ƴan kabilar a muhimmin matsayi a hukumomin ƙasa da kasa Dakta Ngozi Okonjo-Iweala a Matsayin Babban Darakta a Ƙungiyar kasuwanci na Duniya WTO, da kuma Dakta Chikwe Ihekweazu, Mataimakin Babban Darakta a Hukumar Health Emergency Intelligence, na Ƙungiyar lafiya ta Duniya WHO.
Cikin jawabin sa, Shugaban Ƴan kabilar Ibo na Duniya Farfesa George Obiozor, ya bada tabbacin cigaba da samun goyon bayan Ƴan kabilar Ibo ga Shugaban kasa.
"Al'umman Ibo suna goyon bayan hadin kai, kuma akwai labarin wasu Nason ganin sun ture mu wajen Najeriya.
"Al'umman Ibo a Najeriya sun kasance ne kamar kifin cikin teku, ko ta yaya tekun ya juya bazai iya cire kifin daga cikin tekun ba.
"Shugaban Ƙasa, kan wannan batu, munga wanzuwan wani abun Alkhairi a Ƙasar Ibo kuma munyi imani cewa, daka koma Abuja daga wannan ziyara zai kafa tushen samun wani Dandali daza tattauna Muhimman abubuwa da suka shafi Kasar Ibo." a Cewar sa.
managarciya