Bayanan da DCL Hausa ta samu daga jihar Zamfara sun ce barayin daji sun yi awon-gaba da shugaban karamar hukumar Bungudu Hon Nura Abdullah, matarsa da ‘ya’yansa biyu a gidansa da ke Bungudu.
Haka kuma, DCL Hausa ta samu cewa ɓarayin dajin sun yi ajalin ‘yan sanda biyu da ke gadin gidansa da ɗan banga ɗaya bayan mutanen gari da lamarin ya shafa.
Sai dai rahotanni sun ce daga bisani ‘yan bindigar sun sako matar dan siyasar da ‘ya’yansa.
Jami’an tsaro na su yi magana kan lamarin ba.






