Home Labarai ‘Yan bindiga sun yi Garkuwa Da ɗalibbai 7 na  Kwalejin Ƙereƙere a...

‘Yan bindiga sun yi Garkuwa Da ɗalibbai 7 na  Kwalejin Ƙereƙere a Zamfara 

21
0

‘Yan bindiga masu yawa sun yi garkuwa da ɗalibban Kwalejin Fasaha da ƙere-ƙere ta tarayya dake karamar hukumar Ƙaura Namoda  su bakwai a daren Talata, a jihar Zamfara.

Ɗalibban da suke kwana a ɗakunan ɗalibbai na wajen makaranta da ake karɓa haya, ‘yan bindigar sun yi awon gaba da su domin neman kuɗin fansa.

Majiyar da ta shedawa Aminiya ta ce 

an yi garkuwa da ɗaliban Federal Polytechnic Ƙaura Namoda 7 maza a ɗakunan kwanan su a daren jiya Talata, ba tare da an zubar da jini ko samun tirjiya ba.

Jami’in kula da ɗalibbai a kwalejin Aminu Ibrahim ya ƙi aminta ya ce komai kan garkuwa da ɗalibbansu da aka yi, ya ce  shi ba ya da hurumin magana kai.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan Zamfara Yazid Abubakar ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce “ɗalibban ba a cikin Polytechnic suke kwana ba, suna zaune ne a cikin ɗakunan da aka yi a wajen makaranta, abin ya faru da su gaskiya, ɗaya daga cikin su (ɗalibban) ya samu nasara ya gudu, yanzu haka mutanenmu sun ba zama don a tabbatar an kuɓutar da waɗanda ke hannu su shida.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here