'Yan bindiga sun yi garkuwa da ɗalibin jami'a

'Yan bindiga sun yi garkuwa da ɗalibin jami'a

Rundunar ƴan sanda ta jihar Cross River ta tabbatar da sace wani ɗalibin jami’ar Arthur Jarvis da ke Akpabuyo a kusa da Calabar.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Irene Ugbo ce ta tabbatar da faruwar lamarin a wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai Ƙasa, NAN ta wayar tarho a yau Laraba a Calabar.

Ɗaliban na tsaka da komawa ɗakunansu ne daga inda suka je karatu, sai kawai ƴan bindiga suka far musu da misalin karfe 8 na dare a jiya Talata.

Yayin da ƴan bindigar suka kama ɗaya daga cikin ɗaliban, wasu kuma da suka gudu domin tsira da rayukansu, sun samu raunuka daban-daban.

Misis Ugbo ta ce kwamishinan ‘yan sanda, Aminu Alhassan, ya shirya dakarun yaƙi da garkuwa da mutane da su dakile yunƙurin karya doka da oda da kuma tabbatar da kuɓutar da dalibin da aka sace.

Ta ce ‘yan sanda sun fara bincike kan lamarin.

Mukaddashin magatakardar jami’ar, Ngozi Ughas, a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce shugabannin jami'ar sun tashi tsaye kan lamarin.