'Yan bindiga sun sace shugaban malamai da wasu mutane a Zamfara

'Yan bindiga sun sace shugaban malamai da wasu mutane a Zamfara
 

Yankin Arewa maso Yamma na ci gaba da shan fama da hare-haren yan bindiga babu kakkautawa. 

Da yammacin jiya Talata 7 ga watan Oktobar 2024, ‘yan bindiga suka tare hanyar Gusau–Gummi a Jihar Zamfara, inda suka sace mutane da dama. 
Shafin Bakatsine da ke kawo ragotanni kan matsalolin tsaro a manhajar X ya ce miyagun sun dakatar da motoci sannan suka sace fasinjoji. 
Jihar Zamfara na daga cikin jihohi mafi shan fama da matsalolin hare-haren yan bindiga da ya fi shafar yankunan karkara. 
Ba dare, ba rana kullum mahara kara kai hare-hare suke yi cikin sabon salo duk da kokarin da wasu garuruwa musamman a Katsina ke yi na tattaunawa da su. 
A jihar Katsina mai makwbtaka da Zamfara, ƙananan hukumomi da dama sun zauna da maharan domin sulhu da kuma dakile yawan hare-hare a yankunansu. 
A kwanakin baya, Gwamna Dauda Lawal na Zamfara ya yi wasu irin maganganu game da rashin tsaro wanda ya sanya shakku a yaki da ta'addanci. 
Dauda Lawal ya ce a yanzu haka ya san mabuyar yan bindiga da abubuwa da dama game da ayyukansu amma bai isa ba sojoji da yan sanda umarni ba. 
Maganganun sun jawo ce-ce-ku-ce da wasu ke tabbatar da cewa gwamnati ba ta shirya kawo karshen yan ta'adda ba musanman a Arewacin Najeriya. 
Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa, ‘yan bindigar sun kwashe lokaci suna binciken motoci kafin su tafi da mutane da suka kama. Cikin wadanda aka sace akwai Malam Sadis Isa, shugaban malaman Musulunci a ƙaramar hukumar Gummi, abin da ya jawo fargaba a yankin. 
"Da yammacin jiya Talata, ’yan bindiga sun tare hanyar Gusau–Gummi a Jihar Zamfara. 
"Maharan sun dakatar da motoci sannan suka sace fasinjoji da dama, ciki har da Malam Sadis Isa, shugaban Majalisar Malamai ta karamar hukumar Gummi.
A baya, mun kawo muku labarin cewa 'yan bindiga sun kai wani hari a Tsauni da ke birnin Gusau a jihar Zamfara inda suka sace kansiloli biyu yayin farmakin. 
Lamarin ya faru ne da dare inda aka dauke kansilolin biyu daga karamar hukumar Maradun da wani liman bayan sallar Magriba.