'Yan Bindiga  Sun Sace Sarki  Da Matarsa A Nasarawa  

'Yan Bindiga  Sun Sace Sarki  Da Matarsa A Nasarawa  

 

Masu garkuwa sun sace sarkin Gurku, Jibrin Mohammed a fadarsa tare da matarsa a jihar Nasarawa. 

An sace babban sarkin ne a jiya Lahadi 6 ga watan Agusta da dare a fadarsa da ke garin tare da mai dakinsa a karamar hukumar Karu da ke jihar.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Rahman Nansel shi ya bayyana haka ga gidan talabijin na Channels a yau Litinin 7 ga watan Agusta. 
Ya ce sun samu labarin sace sarkin ne a fadarsa da ke yankin Mararraba a cikin karamar hukumar Karu da ke jihar. 
Rahman ya ce sun tura jami'an tsaro da 'yan kungiyar sa kai a cikin dazukan yankin don ceto sarkin da iyalinsa, Politics Nigeria ta tattaro. 
Har ila yau, ya tabbatar da cewa ba a samu nasarar ceto wadanda aka sacen ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto. 
A kokarin ceto sarkin da iyalinsa, an kara tura jami'an 'yan sanda da kuma bangaren kwararru na hana garkuwa zuwa dazukan don kwato wadanda aka sacen, cewar Punch. 
Jihar Nasarawa na fama da hare-haren 'yan bindiga musamman a yankunan karkara da ke jihar. A kwanan nan 'yan bindiga sun kai hari gidan tsohon minista Labaran Maku a lokacin mulkin Goodluck Jonathan tare da raunata mutunre da dama.