‘Yan bindiga sun sace mutane da dama bayan kashe mutum 2 a Sakkwato

‘Yan bindiga sun sace mutane da dama bayan kashe mutum 2 a Sakkwato

‘Yan bindiga sun sace mutane da dama a kauyen tsululu kan hanyar su ta zuwa Sakkwato daga karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sakkwato bayan sun harbe direban mota abin da ya yi sanadin rasuwarsa a ranar Laraba.

"Maharan a jiya Talata sun kashe mutum daya sun tafi da daya a garin Gatawa bayan sun yi musayar wuta tsakanin su da jami'an soji tun da safe har dare in da 'yan bindigar suka samu sa'ar kone motar soja daya," a ta bakin wata majiyar.

Ya ce "Sojojin ba su yi nasara kan maharan ba, motar sojan ta kafe jami'an suka barta suka shiga wata anan ne 'yan bindigar suka fito bayan wucewar sojan suka kone ta a gefen garin Gatawa."

Haka ma a yau Laraba 'yan bindigar sun tare hanyar Bafarawa zuwa Shanawa akaramar hukumar Isa suna karbar kudi a hannun 'yan kasuwar da za su tafi cin kasuwa a karamar hukumar Shinkafi.

Majiyayar ta ce duk wanda aka karbi kudinsa a hakan yake tafiya cin kasuwar baya fasawa don ganin suke gara su tafi kasuwar da su koma gida.

Ya ce 'Yan bindigar suna cin karensu ba babbaka a gefen, ba tare da wata takura da ake yi masu ba.

Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin jam'in hulda da jama'a na rundunar sojoji yanki na takwas dana 'yan sanda reshen jiha ASP Ahmad Rufa'i amma hakar ba ta cimma ruwa ba.