Home Labarai ‘Yan bindiga sun sace Amarya da wasu mutum 9 a Sokoto

‘Yan bindiga sun sace Amarya da wasu mutum 9 a Sokoto

17
0

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mutum tara, ciki har da wata amarya, a ƙaramar hukumar Goronyo da ke Jihar Sokoto.

Wani mazaunin yankin ya tabbatar wa ATS cewa, ‘yan bindigar sun kai hari ƙauyen Illela-Dawagari da misalin ƙarfe 12:00 na dare, inda suka kashe mutum ɗaya tare da yin garkuwa da mutum tara, ciki har da amarya.

Ya ce ‘yan bindigar sun aiko da wasu jarirai a gida, amma suka tafi da iyayensu.

A tattaunawarsa da ATS, mazaunin yankin ya koka kan ƙarancin jami’an tsaro a ƙauyukan Goronyo, inda ya buƙaci gwamnatin tarayya da ta Jihar Sokoto su ƙara tura jami’an tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Matsalar rashin tsaro na ci gaba da addabar wasu ƙananan hukumomin gabashin Jihar Sokoto, musamman Sabon Birni, Isa, Goronyo, Rabah da Wurno. Sai dai mazauna yankin sun ce an samu sauƙi a Illela da Gwadabawa idan aka kwatanta da sauran wuraren.

Ya zuwa yanzu, babu wani bayani a hukumance daga hukumomin tsaro ko gwamnatin jihar kan wannan sabon harin da aka kai a ƙauyen Illela-Dawagari da ke ƙaramar hukumar Goronyo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here