‘Yan bindiga sun sace alkalin babbar kotun jihar Kebbi
Wasu da ake zargin ‘yanbindiga ne sun sace wani alkalin babbar kotun Jihar Kebbi, Mai Shari’a Faruku Hassan Bunza, a gidansa da ke kan titin Zogirma a karamar hukumar Bunza kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 12:00 na dare tsakanin Asabar da Lahadi, jim kadan bayan alkalin ya dawo daga wata tafiya daga jihar Sokoto.
Wata majiya ta bayyana cewa maharan sun kutsa cikin gidan tare da tafiya da alkalin, yayin da suke ta harbe-harbe domin razana mutane. Ta ce babu wani daga cikin iyalansa da ya samu rauni.
Majiyar ta kara da cewa an sanar da hukumomin da suka dace da kuma shugabannin babbar Kotun jihar nan take bayan faruwar lamarin.
Kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Kebbi, SP Bashir Usman, ya tabbatar da sace alkalin, yana mai cewa Kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Umar Muhammad Hadejia, ya tura jami’an rundunonin musamman da na tattara bayanan sirri domin ceto alkalin cikin koshin lafiya.
Ya ce jami’an tsaro na ci gaba da gudanar da bincike tare da sintiri a wuraren da ake zargi, ciki har da dazuka, domin ganin an kubutar da alkalin ba tare da wata illa ba.
Wani babban jami’in Babbar Kotun Kebbi, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici ga bangaren shari’a, yana mai cewa tuni mahukuntan kotun suka gana da shugabannin hukumomin tsaro domin tsara matakan ganin an sako alkalin cikin gaggawa.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, babu wata kungiyar da ta dauki alhakin sace Mai Shari’a Faruku Hassan Bunza.






