’Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 40 A Jihar Kebbi Da Zamfara

’Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 40 A Jihar Kebbi Da Zamfara

Akalla mutum 40 ne ’yan bindiga suka kashe, ciki har da jami’an tsaro, a jihohin Kebbi da Zamfara a ranar Lahadi.

Daga cikin mutanen da aka kashe har da ’yan sandan kwantar da tarzoma shida da fararen hula 36 a kauyen Dan Umaru da ke Karamar Hukumar Zuru a Jihar Kebbi.

Mazauna yankin sun shaida wa wakilinmu cewa an gudanar da jana’izar mutum 27, wasu mutane da dama kuma sun samu raunuka a harin.

Sun bayyana cewa maharan sun kuma sace mutane da daruruwan dabbobi a kauyukan da ke makwabtaka da su.

A Jihar Zamfara kuma an kashe wasu mutum uku a wani kauye da ke Karamar Hukumar Shinkafi.

Sai dai har zuwa lokacin da muka kammala rubuta wanann labarin, hukumomin ’yan sanda ba su fiar ta bayani kan lamarin ba.