'Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 28 A Wani Kauyen Jihar Sakkwato

'Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 28 A Wani Kauyen Jihar Sakkwato

 

Daga Jabir Ridwan Sokoto.

 

Wasu da ake zargi Yan bindiga ne sunkai wani mummunan hari a kauyen Duma Dake karamar hukumar Tureta Dake Jahar Sokoto, inda akalla mutum 28 suka rasa rayukansu.

 

Gwamnatin jahar sokoto itace ta tabbatarda faruwar lamarin tareda bayyana adadin wadanda suka rasa rayukansu a ranar juma'a.
 
Rahotanni sun bayyana cewa, harin ankaishi ne tun a daren ranar laraba, inda Yan bindigar suka
mamaye kauyen tareda yin gaba da dabbobi da dama.
 
Hakama jaridar solacebase ta ruwaito cewa Yan bindigar sunyi garkuwa da mutane da dama yayin qaddamar da harin.
 
ext-align: justify;">Wani mazauni kauyen Mai suna Garba Mailambu  ya shaidawa kamfanin dillancin larabai na kasa NAN cewa, Yan bindigar sunzo ne akan babura inda Suke ta Harbin ka Mai uwa da wabi, ya Kara da cewa wasu mazauna kauyen a yayin gudun tsira da rayukansu wadansu da dama sun afka cikin gulbi.
 
Shima wani mazauni kauyen ya bayyana cewa Yan bindigar sun tusa qeyar wadanda sukayi garkuwa dasu mafiyawan su Kuma matasa domin su kora musu dabbobi zuwa wajen gari.
 
Hakama Yan bindigar sun bukaci man fetur Mai yawa a matsayin kudin fansa domin Sako wadanda sukayi garkuwa dasu.
 
Bayan faruwar lamarin gwamnan jahar sokoto Aminu waziri tambuwal yakai ziyara a kauyen da lamarin yafaru domin jajan ta musu.
 

Abin jira a gani shine wani mataki gwamnati zata dauka don kubutar da wadanda akayi garkuwa dasu, tareda shawo kan matsalar satar mutane da Kuma kisan al'umma da yakici yaki canyewa.