'Yan bindiga sun kashe masunta 3 a Sakkwato 

'Yan bindiga sun kashe masunta 3 a Sakkwato 
'Yan bindigar Lakurawa sun kai hari a kauyen Sanyinna dake cikin karamar hukumar Tangaza a jihar Sakkwato in da suka kashe wasu masunta guda uku a wannan Talata.
Majiyar a cikin kauyen ta ce 'yan bindigar sun kashe mutanen ne a lokacin da suka kawo hari da safe Talata yayin da mutanen suka fita neman abinci waton kamun kifi.
Haka ma 'yan bindigar sun kai hari a jiya  Litinin a garin Sutti da Takkau duk a karamar hukumar sun jikkata mutum biyu.
Mataimaki na musamman ga shugaban karamar hukumar Tangaza  kan tsaro Alhaji Gazali Raka ya tabbatar da faruwar lamarin ya kara da cewar 'yan bindigar sun sace dabbobi da suka kunshi Shanu da Rakumma da Tumaki da Akuyoyi.
Alhaji Raka ya jinjina wa jami'an tsaro kan gaggawar daukar mataki da suka yi har suka kori 'yan bindigar tare da kwato dabbobi a kauyen Siddi.
Mutum biyu da suka samu rauni ta hanyar harbi suna a babbar asibitin Tangaza suna karbar magani.
Raka ya bayyana damuwarsa yadda hari ke karuwa a garuruwansu musamman a cikin yini, 'yan bindigar sun damu duk in da dabbobi suke su kai harin.
Raka ya yi kira ga gwamnatin tarayya da jiha su kara kaimi don ganin sun dawo da zaman lafiya a yanki don samar da cigaba mai dorewa.