'Yan bindiga sun kashe masallata da dama a Sakkwato

'Yan bindiga sun kashe masallata da dama a Sakkwato

 

An shiga tashin hankali bayan kai wani mummunan harin 'yan bindiga a jihar Sakkwato in da harin 'yan ta'ddar ke kara ta'azara a fadin jihar.
 
A kowace shekara a lokacin Damina 'yan bindiga na kara kai hari da tayar da jama'a a garuruwansu da hana masu noma a gona da kara sanya masu haraji kamar kowane lokaci a wannan shekarar ma suna ci gaba da wahalar da mazauna kananan hukumomi 20 daga cikin 23 da jihar ke da su.
 
Majiyoyi sun tabbatar da cewa maharan sun hallaka wasu mutane da dama kuma suka yi garkuwa da wasu sun shiga  daji da su.
 
Shafin Bakatsine da ke kawo rahotanni da suka shafi matsalar tsaro  ya tabbatar da haka a manhajar X a yau Lahadi.
 
 'Yan bindiga sun kai hari a masallaci a an  tabbatar sun sace mutane da dama.
 
Maharan sun afka wa wani masallaci a garin Bushe na ƙaramar hukumar Sabon Birni, inda suka sace akalla mutum 10, ciki har da liman. 
 
Rundunar ’yan sandan jiha ta tabbatar da faruwar lamarin, tare da bayyana cewa ana kokarin ceto mutanen da 'yan bindigar suka sace. 
 
Wani dan majalisar dokokin jihar ya yabawa sojoji bisa hana ’yan bindigar yin garkuwa da karin mutane bayan sun kai mummunan harin.
 
Haka kuma majiyoyi sun ce maharan sun sake kai hari  ana tsaka da sallar Isha a kauyen Marnona dake cikin karamar hukumar Wurno adaren Assabar data gabata.
 
An tabbatar da cewa maharan sun hallaka masallata da dama sannan suka kwashe wasu daga cikinsu zuwa cikin daji domin neman kuɗin fansa.
 
Sanarwar Bakatsine ta ce: Jiya da daddare, ’yan bindiga sun kai wa masu ibada hari yayin sallar Isha’i a kauyen Marnona, karamar hukumar Wurno, jihar Sakkwato. 
 
"An harbe wasu daga cikin masu ibadar, sannan kuma an yi garkuwa da wasu da dama aka tafi da su cikin daji." 
 
Sanata mai wakiltar yankin Sakkwato ta gabas a majalisar dattijai Sanata Ibrahim Lamido ya jajantawa mutanen da lamarin ya faru da su a Kauyen Bushe da Marnona, tare da kira ga hukumomi da kara tashi tsaye wajen kare ruyuwa da dukiyar al'umma.
 
Sanata Ibrahim Lamido ya ce wannan lamarin da ya ke ta faruwa a yankin da yake wakilta akwai bukatar kara kaimi a wajen jami'an tsaro da gwamnatin jihar Sakkwato ganin yanda lamarin tsaron ke kara tabarbarewa a a yankin da jiha baki daya.
 
"Ni Allah ya sani ban tsaya ina kallon wannan lamari ba ina daukar matakan da yakamata dan majalisa ya dauka, kuma a haka nake fatan a samu daidaituwar lamari musamman a yankin namu, kuma ba zan tsaya ba har sai an samu nasara dawo da tsaro a cikin al'umma."