Home Rahoto ‘Yan bindiga sun kashe Hakimin garin Dalijan a Sakkwato

‘Yan bindiga sun kashe Hakimin garin Dalijan a Sakkwato

16
0


‘Yan bindiga sun kai farmaki ga al’ummar Dalijan dake mazabar Jamali a karamar hukumar Binji a jihar Sakkwatosun kashe hakimin garin Alhaaji Ibrahim Magaji Tanko, a ranar Alhamis data gabata.

Maharan bayan sun kashe maigarin sun sace dabbobi da suka hada da Shanu da Awaki da Tumaki da Kaji da kayan abinci da abubuwan amfanin gida.

Karamar hukumar Binji tana da iyaka da kananan hukumomin Tangaza da Gudu in ‘yan bindigar Lakurawa suka yi kakagida.

Bayanan wadanan maharan ne ya haifar da matsalar tsaro a Binji in da batagarin ke yin abubuwan barna da suka shafi garkuwa da mutane da fashi da makami da satar dabbobi.

Shugaban karamar hukumar Binji Alhaji Dikko Nabunkari ya yi tir da faruwar lamarin ya kuma mika ta’aziyarsa kan kisan  uban kasar.A bayaninsa Nabunkari ya roki Allah ya gafartawa mamacin ya kuma yi kiran al’ummar yankin da su kwantar da hankali.

“Allah ya gafarta masa iyalai da masoyansa ya ba su juriyar a wannan lokaci da wannan musiba ta same mu.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here