'Yan Bindiga Sun Kashe Basarake a Sokoto, Mutanen Gari Sun Tsere daga Gidajensu 

'Yan Bindiga Sun Kashe Basarake a Sokoto, Mutanen Gari Sun Tsere daga Gidajensu 

 
'Yan ta'adda da ake zargin Lakurawa ne sun kai sabon hari a ƙauyen Sayinna da ke ƙaramar hukumar Tangaza ta jihar Sokoto.
A yayin harin, an ce miyagun sun hallaka hakimin Sayinna da wani mazaunin garin, yayin da suka tafka barna mai mugun yawa a kauyen.
Zagazola Makama, ya rahoto a shafinsa na X cewa, 'yan bindigar sun kai hari ƙauyen Sayinna ne da misalin ƙarfe 1:30 na daren ranar Alhamis, 18 ga Satumba, 2025. 
Mai sharhi kan lamuran tsaron, wata majiya ta shaida masa cewa maharan dauke da miyagun makamai sun kutsa cikin ƙauyen, suka fara harbi kan mai uwa da wabi. Majiyar ta ce 'yan ta'addan sun harbe mutane biyu har lahira – Murtala Sa’adu mai shekaru 47, wanda shi ne hakimin ƙauyen Sayinna, da kuma Ibrahim Mai-Kudi. “Bayan kisan, ‘yan ta’addan suka arce cikin dazuka da ke kusa da ƙauyen,” in ji majiyar.
Dakarun Operation FANSAN YANMA sun isa wurin domin ceto al’umma, inda suka ɗauki gawarwakin zuwa asibiti tare da fara sintiri a yankin domin hana sake faruwar hari. Karuwar hare-haren Lakurawa a Sokoto Sai dai harin Sayinna na ɗaya daga cikin jerin hare-haren Lakurawa da suka addabi Sokoto kwanan nan, cewar rahoton jaridar Vanguard.
Rahoton ya nuna cewa mayakan Lakurawa sun kai hari ƙauyuka da dama a Kebbe da Tambuwal, inda suka lalata gidaje, suka yi fashi da makami, tare da tilasta al’umma yin gudun hijira. 
A karamar hukumar Kebbe, ƙauyuka kamar Fakku, Sha’alwashi, Tulluwa, Bashi Bakin Dutse, da Rafin-Gora sun fara komawa tamkar kufai.
An ce maharan sun ƙona gidaje, sun sace kayayyaki, suka kuma jefa fargaba ga mazauna garuruwan, wanda ya tilasta su yin hijira. Lamarin ya tilasta hakimin wa Fakku da iyalansa tsere zuwa garin Koko da ke jihar Kebbi, inda suka shiga sahun daruruwan masu gudun hijira.