Home Rahoto ‘Yan bindiga sun hallaka mutane 17 a Sakkwato 

‘Yan bindiga sun hallaka mutane 17 a Sakkwato 

15
0

A ƙalla mutum 17 ‘yan bindiga suka kashe ciki har da bakwai ‘yan yawon sallah a wani hari da aka kai a ƙauyen Ɗangulbi a ƙaramar hukumar Tureta ta jihar Sakkwato.

Mazauna garin sun shaidawa manema labarai maharan sun zo da makamai masu haɗari suna kan babura kusan 150 a haka suka shiga garin da safen Lahadi nan take suka riƙa halbin mutane, suka yi sata a shaguna, abin da ya sanya da yawan mutane suka shiga daji da yake kusa da garin.

Majiyar da ta nemi a sakayata kan tsaro ta ce sun zargi ‘yan bindigar su ne da suka baro garin Bagega a ƙaramar hukumar Anka a jihar Zamfara ɗaya daga cikin maɓoyarsu babba.

A cewarsa maharan sun taso ne kan hanyar Barayar Zaki maƙwabtan ƙaramar hukumar Bukuyum kafin su zo ƙauyen Gizazza in da suka yi zaman su a daren kafin sukai hari.

“Mun samu bayani kan zirga-zirga su a ranar Lahadi, sun zo ne daga Bagega suka wuce ta Barayar Zaki suka tsaya Gizazza, daman in dai za su kai hari a ƙauyukkanmu sukan tsaya nan da dare sai wuce da safe,”a cewarsa.

Majiyar ta ce maharan sun shiga Ɗangulbi 10 zuwa 11 na safen Lahadi kai tsaye suka rika halbi kan mai uwa da wabi, mutane suka yi ta gudun neman tsira amma sun kashe mutane 17 a harin,” in ji shi.

Wasu daga cikin waɗanda lamarin ya rutsa da su akwai Mune, Nagoma, Abdullahi, Danbala, Munden Chana, Muhammadu Dan Amo, Hassan, Abubakar Danbaba and Yidi Bafillace.

Mutane biyar daga ciki ‘yawon sallah ne sun daga Adarawa karamar hukumsr Gummi ta jihar Zamfara, biyu sun zo daga Gidan Gambo a karamar hukumar Shagari, haka ‘yan bindigar sun bata lokaci a kauyen domin su hana  a gudanar da jana’iza ga mutaen da suka kashe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here