'Yan Bindiga Suka Dawo Titin Kaduna-Abuja, Sun Sace Mutum 30 

'Yan Bindiga Suka Dawo Titin Kaduna-Abuja, Sun Sace Mutum 30 

 

'Yan bindiga sun farmaki matafiya a kan titin Abuja zuwa Kaduna a ranar Lahadi, inda suka yi gakuwa da mutum sama da 30.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa wadanda abun ya afku a kan idanunsu da shugabannin yankin sun sanar da ita hakan a ranar Litinin, 8 ga watan Janairu. 
An yi garkuwa da mutanen ne a Dogon-Fili kusa da Katari, hanyar titin Kaduna zuwa Abuja a karamar hukumar Kachia ta jihar Kaduna. 
Wannan shi ne karon farko cikin sama da watanni goma da aka yi kutse ga tsaro a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna. Bincike sun nuna cewa lamari irin haka da ya faru na karshe ya kasance a ranar 1 ga watan Maris, 2023, lokacin da aka yi garkuwa da mutum 23.