Daga Hussaini Ibrahim, Gusau
Shugaban kungiyar masu Noman masara na jihar, Zamfara, watau (MAN) Alhaji Abdullahi Kwanda, yayi kira ga gwamnatin tarayya da ta cire tallafin man Fetir ta maida shi ga sashen Noma musamman takin dan tallafin abinci yafi mahimmanci akan na man Fetir.
Abdullahi Kwanda ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke tattaunawa da wakilin mu a Gusau babban birnin jihar Zamfara.
Nakwada ya kara da cewa, bilyoyin nairori da gwamnati ke badawa wajan dauko man fetir da gwamnati zata badasu wajan takin zamani lallai da munciyar da afunka baki daya, arzikin kasar mu zai bunkasa fiye da yadda bamuyi tsammani. dan Taki zai wadata manoma zasu samu taki cikin farashi mai sauki, matasa zasu samu abunyi rani da damuna. kuma zai rage zaman kashe wando ga matasa kuma zaitaimaka wajan samar da tsaro. kuma aikin gona rigakafine ga matasa wajan dogara dakai. Kuma zaisamar da ingantacan dawamamen zaman lafiya. dan idan matasan mu basu da aikinyi, abu mai saukine su fada a harkar da bata dace da su ba. Inji Shugaban manoman masara na jihar Zamfara.
Ya ya koma kan batun manyan ‘yan kasuwa kuma masu sana’ar saida taki Shugaban yayi kira a garesu da su samar da kamfanoni sarafa taki a cikin wannan gida Kasa tamu ta yadda babu bukatar sayan takin zamani na qasashen wake. Dan yanzu haka akwai Kamfanini da keyin takin zani mai inganci a Kasar nan wanda Kananan manoma zasu yi amfani da shi kuma su samu amfanin mai inganci.
Haka kazalikama idan gwamnatin jahohi masu kamfanin taki zasu tada kamfanonin su zasu iya samar da taki ga manoma da zasuyi amfani da shi acikin sassaukan farashi. asamar da abuncin da ba’ayi tsamaniba.
A karshe Abdullahi Kwanda yayi kira musamman ga manoman Masara da kada tsadar taki ta basu tsoro a Noman bana ya kamata suyi amfani da takin gargajiya da kuma takin da ake ayinsa anan kasar mai saukin farashi kuma yana da Inganci sosai wajan gudanar na noman su. dan yanzu haka akwai shiri na musamman da Uwar Kungiyar ta masu Noman Masara keyi, Karkashin jagoranci Shugaban ta na Kasa, Alhaji Bello Annur, dan sambar wa mambobin kungiyar hanyoyin cigaban noma na zamani.





