Abubuwan da Ake Bukata su ne:
1. Powdered Milk
2. Condensed Milk
3. Plain Yoghurt
4. Food Color (Pink)
5. Strawberry Flavor
6. Boiled Water
7. Bowl
8. Whisk
Na Saka Matakan acikin Hotunan domin saukin Fahimta, Kuma a Karshen Rubutun akwai Link Wanda zai kaika/ki YouTube domin kallon Yanda Akeyi A aikace.
Mataki Na Farko:
Zaka/ki Dafa Ruwan Zafi sai ka/ki juye a Bowl Dinka/ki. Sai ka/ki Zuba Powdered Milk Dinka/ki aciki tareda Juyashi sosai ta Hanyar amfnai da Whisk (domin kada a bari ya dunkule).
Mataki Na Biyu:
Sai ka/ki ajiye Ruwan yayi Sanyi Tukuna (Tsawon 20minutes a Misali). Zakiga wani Maski ya Kwanta a sama, sai ka/ki Saka cokali ka/ki cire wannan Maskin (Ba'a Bukatar shi).
Mataki Na Uku:
Bayan ya cire zafi, sai ka/ki Zuba Plain Yoghurt Dinka/ki aciki tareda Juyashi sosai ta Hanyar amfani da Whisk har sai ka/kin Tabbatar ya gama hadewa. Sannan sai ka/ki Samu Leda Mai kyau ka rufe Bakin Bowl din sosai tareda Saka murfi a rufe (a Tabbatar iska baya shiga). Sannan sai a saka a Polythene Bag a rufe. Ana iya ajiyewa Tsawon Awanni 16hrs ko Kuma a barshi ya Kwana.
Mataki Na Hudu:
Bayan ya Kwana sai ka/ki dauko ka/ki duba, zakuga ya zama kamar Yoghurt. Daganan sai mu shiga Mataki Na Gaba.
Mataki Na Biyar:
A wannan Matakin Zaka/ki Kara Juyashi sosai (domin alokacin zaka/ki sameshi yayi Kauri Sosai ya cure wuri Daya) har sai ka Tabbatar ya dawo Ruwa. Sannan sai Ka/ki Zuba Condensed Milk Dinka/ki aciki ka Juya Sosai.
Mataki Na Shida:
Sai ka Zuba Food Color (pink) Dinka/ki (a kula kada Yayi Yawa). Shima ka Tabbatar ya Game kowannen bangare (Ba'a so Wani Wurin yayi kala, Amma Wani Wurin Yana Fari). Daganan sai ka/ki Zuba Strawberry Flavor Dinka/dinki dai-dai Bukata, Shima a Juyashi sosai a Tabbatar ya Hade kowanne 6angare.
Mataki Na Bakwai.
Sai ka/ki juye a Goranka/ki, daganan sai A Saka a fridge domin yayi Sanyi.
SHIKENAN SAI A SHA TAREDA BISMILLAH.