YADDA ZA KI SAMAR DA CORNFLAKES NA MUSAMMAN DOMIN IYALINKI
MRSBASAKKWACE'Z KITCHEN
CORNFLAKES
INGREDIENTS
Garin masara
Gishiri
METHOD
Da farko zaki samu garin masara ki zuba a roba se ki zuba gishirin ki kaɗan se ki yayyafa ruwa ki cakuɗa karki bari ya yi ruwa da tauri zaki kwaɓa sai ki rinƙa mitsila kina taɓawa ƙwananu kamar kina taɓa daudawa karki taɓa shi ƙananu sosai domin in ya bushe zai ƙanƙance kina yi kina ɗorawa a takaddar ki se ki sa a oven ki gasa shikenan kin gama hajiya zaki rinƙa sha da madara.
Wannan haɗi zai sauwaka maki wurin sayo na kasuwa.
Haɗin zai samar maki nutsuwa sosai don ke ce kika haɗa da kanki kuma kinsan abubuwan da kika yi amfani da su.
Da yawan yara da mata suna sonsa kuma sukan ci bai ishe su ba amma in kin ka yi naki da kanki za ki yi a wadace cikin sauki da garɗi.
08167151176
MRS BASAKKWACE.
managarciya